✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar ‘Yan fansho ta yi zaben shugabanni a Kano

A makon jiya  ne Kungiyar ’Yan fansho ta Ma’aikatan Tarayya ta gudanar da zaben shugabanninta  da za su ja ragamar shugabancinta  na tsawon shekara hudu.…

A makon jiya  ne Kungiyar ’Yan fansho ta Ma’aikatan Tarayya ta gudanar da zaben shugabanninta  da za su ja ragamar shugabancinta  na tsawon shekara hudu.

An zabi Malam Isyaku Umar a matsayin Shugaba  sai kuma Malam Haruna Usman a matsayin Mataimakin Shugaba.

Sauran sun hada da  Sanusi Lawan a matsayin Ma’aji, sai kuma Jamilu Ado a matsayin Odita. Haka an zabi Abdulwahab Lawan da Abdul Lawan Danlami a matsayin Amintattun Kungiya.

A lokacin da yake jawabi yayin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar,   Shugaban Kwamitin Zaben Mista A. A. Williams ya bayyana cewa ya gamsu da yadda zaben ya gudana, lura da yadda masu zaben suka  gudanar da zaben cikin  hadin kai da farin ciki.

Shi ma a nasa jawabin sabon Shugaban Malam Isyaku Umar ya gode wa ’yan uwansa ’yan fansho da suka zabe shi, kuma ya yi alkawarin tafiya da kowa wajen gudanar da ayyukan kungiyar.

A cewar sabon shugaban zai yi duk abin da ya dace wajen ganin an kwato wa  ’yan uwansa ’yan fansho hakkokinsu, ksancewar yawancin ’yan fansho suna fuskantar matsaloli na rahin biyansu garatuti da kudin fanshonsu na wata-wata.