Da Dumi Dumi

Kungiyar ‘Yan Fansho ta zabi shugabanni a Jigawa

Kungiyar  ’Yan Fansho  ta Kasa ta zabi sababbin shugabanninta a Jihar Jigawa.

Zaben wanda ya gudana a karkashin jagoracin Kwamared William Easier, a Cibiyar ’Yan Fansho ta Jihar Jigawa a ranar Litinin da ta gabata a Dutse, babban birnin jihar, an zabi Malam Yusuf Gako, a matsayin shugaba, babu hamayya.

Haka sauran mukaman an zabe su ne babu hamayya da suka hada da Idris Sale Mataimakin Shugaba da Bashiru Musa, Ma’aji da Muhammad Inuwa, Mai Binciken Kudi.

Sauran sun hada da Ubaliyo Garba da Yusuf Garba, Amintattu na daya da na biyu, inda aka rantsar dasu nan take.

Shugaban Kungiyar ta Kasa Mista Sunday O. Omezi wanda ya halarci wajen rantsuwar, ya hori sababbin shugabannin su rike amana da gaskiya su kuma kwatanta adalci tare da jin tsoron Allah.

ADVERTISEMENT
Share