Da Dumi Dumi

Kungiyar Yarbawan Ogbomosho mazauna Kafanchan ta nemi a zauna lafiya

Kungiyar Yarbawan Ogbomosho

Kungiyar Yarbawan garin Ogbomosho mazauna Kafanchan a Jihar Kaduna sun ce a shirye suke don hada kai da duk masu ruwa-da-tsaki da ke yankin don samar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kabilun yankin mabiya addinai daban-daban.

Shugaban Kungiyar Mista James Adetunji ne ya bayyana haka a yayin gudanar da taron ’ya’yansu don taya Najeriya murnar cika shekara 59 da samun ’yancin kai da aka gudanar a makon jiya gabata a Layin Ibadan da ke garin Kafanchan.

Mista Adetunji, wanda ya yaba wa Masarautar Jama’a kan yadda take tafiya da kabilu daban-daban da ke masarautar ba tare da fifita wasu a kan wasu ba, ya jaddada biyayyarsu tare da alwashin ci gaba da bayar da gudunmawarsu wajen samar da hadin kai da zaman lafiya a yankin.

Shi ma da yake nasa bayanin, wani dan kungiyar da ya haura shekara 50 kuma haifaffen garin Kafanchan, Alhaji Ibrahim Salahudeen, ya yi kira ga ’yan Najeriya su yi watsi da nuna bambancin kabila da na addini a tunkari ayyukan ciyar da kasa gaba.

“Dole ne mu yi watsi da bambancin kabila da addini, mu zo mu hada kanmu don tabbatar da manufar gwamnati wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa,” inji shi

ADVERTISEMENT

Shi kuwa Sakataren Kungiyar, Mista Joel Adegboyenga, ya bayyana manufar shirya taron a irin wannan lokaci da cewa don yada ta’adojin da iyayensu suka gadar musu da kuma irin gudunmawar da matasa za su bayar a matsayinsu na kashin bayan al’umma.

“Babu wata al’umma da za ta ci gaba da kare al’adunta ba tare da tana yada shi a tsakanin matasanta ba, don haka muka shirya irin wannan taro don yada ’yan uwantaka da kaunar juna ba tare da la’akari da addinin mutum ko kabilarsa ba,” inji shi.

Share