Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kungiyar Zawarawa ta Gombe ta yi taron wayar da kan mata

Matan da suka halarci taron Qungiyar Zawarawa ta Gombe

Kungiyar Hadin kan Mata Zawarawa ta Jihar Gombe ta yi taronta na farko na wayar da kai da kuma tattauna matsalolin da ke kawo yawan mace macen aure.

Da take jawabi a wajen taron Shugabar Kungiyar ta Jihar, Malama Fatsuma Abdullahi, cewa ta yi sun kafa kungiyar ce don bai wa zawarawa shawarwari kan zaman aure da yadda za a shawo kan matsalar yawan mace macen aure da ke mayar da su zawarawa.

ADVERTISEMENT

Malam Fatsuma Abdullahi, ta bai wa zawarawan shawarwari da cewa, hakuri da juna a gidan miji da hakuri da dan abin da miji zai kawo komai kankantarsa ya fi rashin hakurin saboda yanayin rayuwa da ake ciki. “Rashin hakuri ke haifar da mafi yawan mutuwar aure a tsakanin matan Hausawa da Fulani saboda wadansu matan na ganin sai miji ya musu irin bukatun da yake yi musu a waje kafin aure,” inji Shugabar.

Ta kara da cewa, mace-macen aure ya fi faruwa ne a lokacin da ma’aurata suka gina aure a kan karya, namiji ya yi wa mace alkawarin zai yi mata kaza zai mata kaza ita kuwa idan ta shiga gidan ba ta ga alkawarin da aka yi mata ba sai ta gaza hakuri.

ADVERTISEMENT

Fatsuma Abdullahi, ta yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga sabuwar gwamnati mai jiran gado ta Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, da ta sa kungiyar su a jerin kungiyoyi da ake bai wa tallafi don ganin sun samu dama na koya wa mambobinsu kananan sana’o’i don dogaro da kai kafin su yi aure ya kasance suna da sana’ar da ko sun sake wani auren don miji bai samu ya kawo ba mace za ta kula da gida. Daga nan sai shugabar ta nemi matan su ci gaba da ba su hadin kai don sai da hadin kai ne komai zai gudana yadda ake so.

Malam Sulaiman Adamu, da ya taya mata zawarawan murnar wannan taro inda ya ja hankalinsu cewa su kara hakuri da rayuwa musamman a lokacin zamantakewar aure.

Wadansu zawarawa da suka zanta da Aminiya sun nuna farin cikinsu kan wannan kungiya inda suka ce suna da yakinin kungiyar za ta taimaka musu.

Zawarawa fiye da 300 ne suka halarci taron daga kananan hukumomi 11 na jihar kuma taron ya gudana ne a makarantar firamare ta Bubayero da ke fadar jihar.