✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘kungiyarmu tana mara wa gwamnatin Yobe a yakar cutar shan-inna’

kungiyar masu dauke da nakasa da ke da alaka da cutar shan-inna a Jihar Yobe ta yi alwashin mara wa gwamnatin jihar a kokarinta na…

kungiyar masu dauke da nakasa da ke da alaka da cutar shan-inna a Jihar Yobe ta yi alwashin mara wa gwamnatin jihar a kokarinta na kawar da cutar shan-inna (polio) a tsakanin al’ummar jihar dungurungum.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar, Malam Muhammad Abatcha a tattaunawarsu da Aminiya jim kadan da kammala wani gangamin wayar da kan jama’a da kungiyar ta shirya a Damaturu na neman iyaye su ba da ’ya’yansu don a yi musu alllurar rigakafin cutar ta shan-inna.
Shugaban ya ce halin da suke ciki ya sa suka dage don wayar da kan jama’a na su nisantar da ’ya’yansu kamuwa da wannan cuta ta fuskar amincewa a yi musu allurar rigakafin cutar ta shan-inna, domin ya fi magani.  Yin rigakafin cutar shan-inna zai taimaka wajen samun yara masu lafiya da za su tallafa wa kasa nan gaba, kuma zai taimaka wajen kawar da cutar  a doron kasa.
Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar ta Yobe ta kara kaimi wajen tallafa wa kungiyar tasu a dukkan kananan hukumomin jihar 17, tunda suna da rassa a ko’ina, a duk yayin da za su gudanar da gangaminsu da duk kayayyakin da suka kamata, musamman da yake nasu gangamin yakan karbu ga al’umma fiye da gangamin da wasu da ba su dauke da cutar ke yi, tunda su ne kankat.
Malam Muhammad ya gode wa gwamnatin kan tallafin da ake ba su akai-akai don samar da saukin rayuwa ga ’ya’yan kungiyar, musamman da gwamnatin Gaidam ta tallafa musu da KEKE NAPEP guda 5 da kuma gina musu babban ofis irin na zamani a bakin kasuwar Damaturu. Ya kuma roki gwamnatin ta tsunduma su cikinta ta yadda za su samu wakilci, sannan kuma a rika daukar ’ya’yan kungiyar aiki tunda akwai wadanda suka kammala makarantun sakandare da na gaba da sakandare, amma ba su da aikin yi.
Shi ma shugaban kwamitin gangamin yaki da cutar shan-inna da ke cikin kungiyar nakasassun, reshen karamar Hukumar Damaturu, Malam Muhammad Ibn Ishak cewa ya yi gangamin da suke yi na neman iyaye su fito don ba da ’ya’yansu a diga musu maganin rigakafin, suna shiga ne birni da kauye, kuwa fadakarwar tana karbuwa. Don haka ya nemi iyaye da su ci gaba da ba da hadin kai don ganin an kawar da cutar a fadin jihar da ma kasa baki daya. Ya kuma nemi karamar Hukumar Damaturu ta rika damawa da su a dukkan abin da ya taso, ba wai sai lokacin allurar polio kawai ba.