✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyarmu za ta taimaka wa mata da yara da nakasassu da marasa galihu – Uwargidan Gwaman Kebbi

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya A’isha Atiku Bagudu, ta kafa wata kungiya domin taimaka wa mata da yara da nakasassu da marayu domin dogaro da…

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya A’isha Atiku Bagudu, ta kafa wata kungiya domin taimaka wa mata da yara da nakasassu da marayu domin dogaro da kai. Ta yi albishir ga wadannan rukunin mutane a hirarsu da wakilinmu:

Mene ne dalilin kafa wannan kungiya kuma mene ne sunanta?

Bismillahi rahamani rahim.Da farko wannan kungiya mun sanya mata suna MALLPAI kuma abin da ya sa muka kafa kungiyar saboda mu taimaka wa mata da yara da nakasassu da marasa galihu. Kuma za ka ga a duk lokacin da talakawa suka yi zaben sababbin shugabannin da za su wakilce su a jihohi da tarraya, to za su koma gefe ne kawai suna sauraron irin ababen alherin da za su inganta rayuwarsu ta kowace fuska ganin cewa, wannan shi ne hanyar da talakawa za su ci moriyar dimokuradiyya,

A kan haka ne muke son mu bunkasa harkokin rayuwar mata da kananan yara da marayu da kuma nakasassu duk da cewa wannan kungiya ba ta gwamnati ce ba, ba ta kuma alaka da gwamnati.

Wane taimako ne kungiyarku take yi?

Kungiyarmu tana taimaka wa marayu wajen ba su abinci da  saya musu sutura, kuma muna tura yara zuwa makarantu da dinka musu kayan makaranta. Akwai shiri na musamman da muka fito da shi domin  koyar da  sana’o’i ga mata da yara domin dogaro  da kai, haka su ma nakasassu za mu rika taimaka musu ta kowane bangaren rayuwarsu, idan bukatar haka ta taso.

Muna son kafin nan da shekarar 2020 a kowace hedikwatar karamar hukuma a Jihar Kebbi mu bude cibiyar koyar da sana’o’i ta mata da yara, haka su ma matan aure ba za mu bar su a baya ba.

Ko kuna da wani shiri na taimaka wa mata masu juna biyu?

Na ji dadin wannan tambaya, ai mata masu ciki kusan in ce su ne  a sahun gaba wajen ba su taimako, domin su suke bukatar taimako a cikin gaggawa. Saboda duk taimakon da muke bayarwa ga yara idan iyaye mata ba su haihu aka samu yaran ba, ina za mu ba da taimakon?

Saboda haka yanzu mun fara sayen magunguna domin rarraba wa ga kananan asibitocinmu na karkara domin bai wa mata masu ciki da kuma nakasassu da yara kanana. Kuma a nan gaba kungiyarmu za ta fito da shirin kirkiro da rumbun adana jini domin agazawa da rage yawan mace-macen mata masu ciki da kananan yara saboda rashin isasshen jini.

Ko akwai wani tallafi da za ku yi wa samari matasa musamman ta fuskar ilimi?

Samari matasa ai su ne abin taimaka mawa, domin zuwa karo ilimi. Saboda su ne manyan gobe, kungiyarmu da ma tana da kyakkyawar niyyar ta fuskar daukar yaran da aka kora a makaranta da yaran da suka gudu daga makaranta da wadanda iyayensu suka kasa taimaka musu dalilin rashin abin hannu, wanda wannan ke sa yara wajen aiwatar da aikin assha da zaman kashe wando da shaye-shaye a cikin al’umma.

A matsayinki na uwa me za ki ce game da illar talla ga ’ya mace?

Na san wani lokaci wadansu iyayen kan  nuna cewa su ma ba a son ransu suke sa ’ya’yansu talla ba. Hakan na faruwa ne saboda wasu dalilai da suka sha karfinsu.

Misali, za ka ga mace na rike da  marayu, ba ta mallaki komai ba, haka nan babu mai tallafa mata ita da ’ya’yanta sai Allah. Da wannan dalilin  yakan zamo wa wadansu mata dole su tura ’ya’yansu talla su rika juya dan jarin da suke da shi domin su samu na abinci. Wani lokaci kuma zai iya kasancewa mahaifin yaran na raye amma ba shi da isasshiyar lafiya.

Idan muka juya ta wani fannin kuma sai mu ga mutuwar zuciya da yawan son abin duniya su ke sa wadansu iyaye tura ’yayansu talla. Na kuma fi dora wannan laifi ga iyaye mata. Za ka ga magidanci yana iyakacin kokarinsa wajen biyan bukatun iyalinsa, ya kuma sa ’ya’yansa a makaranta, amma uwarsu ba za ta bar su su yi karatu ba.

Bayan tallafi da kungiyarku ke yi ko akwai wani abu da ke ci muku tuwo a kwarya?

Abin da ke ci mana tuwo a kwarya kuma in Allah Ya yarda za mu yi yaki da shi, babu kamar yadda ake yi wa yara mata fyade. in Allah Ya yarda duk lokacin da kungiyarmu ta samu wanda ya yi fyade za mu tsaya tsayin daka mu ga an hukunta shi ko shi wane ne. Haka ku ma ’yan jarida akwai gagarumar gudunmawar da za ku bayar a kan wannan lamari. Saboda haka kungiyarmu tana neman hadin kanku, ku ma kun zama mambobi domin ba da taku gudunmawar. Domin kun san ita wannan kungiyar ba ta da wata alaka da gwamnati, amma kuma idan gwamnati za ta ba da taimako a shirye take ta karba.

Wane kira kike da shi ga iyayen yara mata da ake tura su zuwa wasu jihohi don yin makarantar allo.

Madalla wannan tambaya ta sosa mini rai, saboda ina son in kara shaida wa iyayen yara cewa na ji jama’a na cewa wai Matar Gwamna tana son ta hana karatun allo na mata. Ni shawara nake bai wa iyayen yara cewa kowa ya rike ’yarsa a gida ya koya mata karatu na addini da na boko kamar yadda iyayenmu suka ba mu karatu.

Domin abin da iyaye za su lura da shi, ita ’ya mace ba kamar da namiji take ba, su kansu yara maza yaya suka kare da irin wahalhalun da suke sha idan sun je makarantar allo, balle mata. Wadansu za ka gan su a gidajen sayar da abinci suna wanke-wanken kwanuka wadansu za ka same su a bakin manyan kantuna da bankuna suna bara da sauran wuraren da jama’a ke hada-hada.

Iyaye ku kasance masu tausaya wa ’ya’yanku, domin su zamo nagari, duk yaron da ya tashi wurin iyayensa ya samu kyakkyawar tarbiyya idan ya girma ya zama wani abu za ka ga ya fi kyautata wa iyayensa sabanin wanda iyayensa ba su san cinsa da shansa ba, dukkanmu iyayenmu talakawa ne. Iyayena ba su taba tsammanin zan zama Matar Gwamna ba, kuma na yi makarantar allo amma a gida gaban iyayena, mun kuma samu kyakkyawar tarbiyya da ladabi ga kuma karatun bokon mun yi kuma duk a gida gaban iyayenmu muka yi.

Ya kamata ’ya mace ta samu tarbiyya daga uwa, musamman ta fannin zaman aure, amma idan ta girma a wani waje ba za ta samu cikakkiyar tarbiyya ba kamar tana wurin mahaifiyarta ba.