Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

kungiyoyi 8,000 ne ke son Jonathan ya sake tsayawa takara –Farfesa Alkali

Mai ba Shugaban kasa Shawar kan Harkokin Siyasa Farfesa Rufa’i Alkali ya ce kimanin kungiyoyi dubu takwas ne suke bukatar Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sake tsayawa takara ba dubu uku da ya fada daga farko ba.
 Farfesa Alkali ya fadi a baya cewa kungiyoyi dubu uku a ciki da wajen Najeriya ne suke nema Shugaban kasar ya tsaya takara a zaben Shugaban kasa da za a gudanar a watan Fabrairun badi.
Kuma nan take ya kafa kwamitin mutum 11 a karkashin Janar A. T. Ibrahim mai ritaya domin tantace kungiyoyin domin tsara ayyukansu.
Wakilan Kwamitin kungiyoyin Magoya Bayan Goodluck din sun hada da Olusola Oke da Nick Eze da William Makinde da Mohammed El-Amin da Nimi Barigha-Amange da A.Y. Ahamad da Lamido Chikaire da Tony Edoh da Baraka Sani da Godson Nnaka, wanda zai kasance sakatare.
Da yake karbar rahoton kwamitin Farfesa Alkali ya ce, sabanin yadda ya fada a baya, akwai kungiyoyi dubu takwas da suke neman Mista Jonathan ya shiga takarar zaben Shugaban kasa, maimakon dubu uku.
 “Kwamitin ya lura daga rahotonsa cewa sabanin matsayinmu cewa akwai kungiyoyi dubu uku da ke neman Shugaban kasa ya tsaya takara, yanzu ya gano akwai kungiyoyi sama da dubu bakwai na masu goyon bayan a fadin kasa da ke kiran Shugaban kasar ya sake tsayawa takara,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Daga farko mun buga fom-fom dubu biyar da muka raba wa kungiyoyin sa-kai da sauran na magoya baya, kuma nan da nan fom-fom din suka kare, sai da muka sake buga guda dubu biyu. Kuma a maganar da nake yi muku yanzu akwai akalla kungiyoyi dubu da suke neman mu tantance su.”
Mukarrabin Shugaban kasar ya ce ofishinsa zai nazarci rahoton kwamitin domin sake tsara kungiyoyin magoya bayan domin kintsa wa kalubalen da ke tafe a kokarin fuskantar zaben Shugaban kasar.
Ya ce, “Muna son tabbatar wa dukkan kungiyoyin ba tare da lura da girmansu ba, daga mai mutum biyu zuwa mai miliyan 20 duk suna da muhimmanci a wurinmu, kuma za mu tafi tare da su.”
Farfesa Alkali ya bukaci kungiyoyin su fara aiki a shiyyoyi da jihohi da kananan hukumomi da mazabun unguwanni. Ya ce, “Su nemo maza da mata da matasa don fuskantar babban aikin da ke tafe.”
Tun farko da yake mika rahoton Janar Ibrahim mai ritaya ya ce, Shugaba Jonathan da jam’iyyarsa ta PDP, su sanya ran fuskantar takara mai zafi a badi, inda ya ce, ’yan adawa a yanzu sun kintsa sosai ba kamar na zabubbukan baya ba.  “Mu sa ran haduwa da adawa mai karfi a zaben 2015, domin ’yan adawa a yanzu suna da karfi ba kamar yadda muke a shekarar 2011 ba. Jam’iyya da fadar Shugaban kasa su fito da dabarun da za su tabbatar Shugaban kasa ya koma kan kujerarsa a shekarar 2015,” inji shi.

ADVERTISEMENT