Kungiyoyi sun ziyarci kurkuku da asibitin Kafanchan

Mambobin kungiyar yayin ziyarar a kurukukun Kafanchan
Mambobin kungiyar yayin ziyarar a kurukukun Kafanchan

Kungiyar Matasan Najeriya ta Kasa (NYC), reshen Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna da Kungiyar Intansurullah Yansurukum sun ziyarci kurukukun garin Kafanchan da ke karamar hukumar a lokuta daban-daban; inda suka kai tallafin sabulai da omo da garin kwaki.

Yayin da yake yi wa fursunonin jawabi, Shugaban Kungiyar NYC na karamar hukumar wanda ya jagoranci ayarin, Kwamared Solomon Samuel ya yi kira ga fursunonin su dauki zamansu a gidan kaddara da kuma wajen da za su kyautata dabi’unsu don zama mutane masu amfani ga kasa gaba daya.

Kwamared Samuel ya yi musu fatar zamowa wadansu fitattun mutane bayan sun fito, inda ya ce, wadansu daga cikin fitattun mutane ciki har da wadansu shugabannin kasa sun yi zaman gidan yari amma bayan fitowarsu sun zamo wadanda duniya ke alfahari da su.

Ya tabbatar musu da cewa kungiyarsu za ta ci gaba da sanya su cikin jadawalin wadanda ba za ta manta da su a dukkan shirye-shiryenta da kuma lokacin da wani taimako ya taso lura da cewa yawancinsu matasa ne masu jini a jiki.

A jawabin Shugaban Kungiyar Intansurullah, Malam Muhammad Kabir ya yi wa tsararrun alkawarin cewa nan gaba kadan za su sake kawo musu ziyara don duba yiwuwar fitar da wadansu daga gidan yarin da laifinsu bai taka kara ya karya ba kuma ana tsare da su ne a kan kudi kadan.

ADVERTISEMENT

Yayin da yake maida jawabi bayan karbar kayayyakin da kungiyar ta kawo da suka hada da kwalayen omo da sabulu, jami’in da ke kula da gidan fursunan, Cif Sufuritanda Mathias Dzuzu ya yaba wa kungiyar kan tunawa da ’yan uwansu da ke gidan kaso da kuma kawo musu tallafi da gabatar musu da jan hankali don kada su cire tsammani daga zamowa mutanen kwarai da za su zamo masu amfani a cikin al’umma.

Daga nan Kungiyar NYCN ta zarce Babban Asibitin Kafanchan ta kai tallafi ga dakunan jinyar kananan yara.

A ci gaba da harkokinta, Kungiyar NYCN ta shirya taron wuni guda kan tasirin ilimi wajen bunkasa ci gaban kasa da al’umma.

Taron, wanda aka gudanar a dakin taro na Sakatariyar Karamar Hukumar Jama’a da ke Kafanchan, ya hada da bayar da kyaututtuka da karrama wadansu fitattun mutane da suka bayar da gudunmawarsu ta hanyoyi daban-daban a karamar hukumar.

Lokacin da yake jawabi, shugaban taro, kuma Shugaban Kwalejin Ilmi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya, Farfesa Aledander Kure, ya yi kira ga iyaye da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar ilimi su rika wayar da kan ’ya’yansu kan makasudin neman ilimi wanda ba ya tsaya ne kawai ga neman aikin gwamnati ba, sai dai don daga darajar mutum tare da ba shi damar kirkira don amfanar kansa da al’ummar da yake ciki da kasa baki daya.

Ya shawarci ’ya’yan kungiyar su rika gabatar da wadansu matasa masu karancin shekaru da suka yi wata bajinta a rayuwarsu a duk lokacin da suka tashi shirya wani biki don sauran matasan su samu abin koyi daga ’yan uwansu.

Shugaban Kungiyar NYCN ta Kasa reshen Jihar Kaduna Kwamared Nathaniel Bagudu ya bayyana takaicinsa ne kan yadda har yanzu Najeriya ke bin tsofaffin hanyoyin koyarwa alhali duniya na ci gaba ta hanyoyin kimiyya da kere-kere.

“Idan mutum yana musu  ya koma kwaleji ko jami’a ko sakandaren da ya kammala shekara 10 da suka wuce don tabbatar wa kansa,” inji shi

Shugaban kungiyar na karamar hukumar, Kwamared Samuel Jatau ya mika kokon bararsu ne ga shugabannin karamar hukumar da sauran masu hali kan su taimaka wa kungiyar da wasu abubuwa ciki har da motar zirga-zirga don saukaka musu ayyukansu.

Yayin da yake bayani, jim kadan bayan rantsar da su, sabon Shugaban Kwamitin Amintattun Kungiyar kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, Mista Ado Dogo Audu, ya sha alwashin tallafa wa kungiyar da shawarwari da sauran abubuwan da suka kamata don su samu damar tallafa wa wadansu nan gaba.

Share