✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Kungiyoyin kwararru sun yi watsi da matsayin kungiyoyin kabilun kan Atiku

Wasu kungiyoyi da suka hada da Kungiyar Kwararru ta Arewa (Northern Alternatibe Forum -NAF) da ta Masana ta Kudu maso Kudu (SSP) da ta Dimokuradiyya…

Wasu kungiyoyi da suka hada da Kungiyar Kwararru ta Arewa (Northern Alternatibe Forum -NAF) da ta Masana ta Kudu maso Kudu (SSP) da ta Dimokuradiyya ta Yankin Oduduwa  (ODG),  da dukansu aka fi sani da “Kungiyoyin Kwararru na Yankunan Najeriya,” sun ce sun barranta daga ayyana dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a matsayin wanda ya cancanci zaman Shugaban Kasa da wasu kungiyoyin kabilu suka yi.

Shugabannin kungiyoyin NAF da SSP da ODG, wadanda suka kira kansu kungiyoyin kwararru na yankunan kasar nan shida sun bayyana haka ne kwana daya da matsayar kungiyoyin kabilu a taron da su ma suka gudanar a Abuja.

Sun mayar da martani ne ga ayyana Atiku Abubakar a matsayin dan takarar kungiyoyin NEFda Ohaneze Ndigbo da MBF da PNDF da (NEF).

Wata sanarwa dauke da sanya hannun Malam Gidado Ibrahim da Dokta Tunji Yekini da Mista Arinze Goodwill da kuma Mista Mbeke Itah, suka fitar ta bayyana amincewa da takarar Atiku da abin da ta kira “shugabannin kabilu” suka yi a matsayin wasan yara, inda suka ce matakin ba ya nuna gaskiyar abubuwan da suke gudana a yankuna shida na siyasar kasar nan. Kungiyoyin sun yi fatali da ayyana Atiku inda suka ce mutane tun daga matakin karkara suna tare da dan takarar Jam’iyyar APC, Shugaba Muhammadu Buhari.

“Muna kira ga dattawanmu su rika taka-tsantsan don kada su mayar da kasar nan kan mugun hannu kamar yadda muka gani a mummunan mulki na shekarar 16 na PDP. Muna kira ga ’yan Najeriya su lura cewa mu ba ma cikin gurbatacciyar siyasar nan da ake kira ayyana dan takara da wadannan masu kiran kansu shugabanni daga shiyyoyi. Mu muna matukar goyon bayan sake zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 16 ga Fabrairun bana. Don haka a yi watsi da nuna goyon baya ga Atiku da kungiyoyin kabilun suka yi,” inji sanarwar.

Ta kara da cewa: “Wadannan fa mutane ne da ba su tare da mutane a can kasa. Kuma suna neman abin da za su wawura ne kafin zaben na 16 ga Fabrairu. Don haka a yi watsi da ra’ayinsu domin jama’a suna tare da Shugaba Muhammadu Buhari saboda nasarorin da ya samu.”

Sun ce suna tare da Buhari ne saboda yadda yake yaki da cin hanci da rashawa da sauran miyagun ayyuka. “An samu juyin-juya-hali game da kudin shiga. Yanzu ana samun nasara inda wasu hukumomin irin JAMB suke samar da makudan kudi kuma talaka yana murmurewa. Don haka muna kira ga ’yan Najeriya su gusa gaba daga yin kamfe a kan titi kadai su fito su nema wa Shugaba Buhari goyon baya domin kawo mafita ga matsalolin Najeriya,” inji su.

A martani da fadar Shugaban Kasa ta mayar kan goyon bayan kungiyoyin kabilun ga Atiku ta ce hakan wata damfara ce ta wadansu ’ya’yan PDP da suke neman mulki ido rufe.

Kakakin Kwamitin Yakin Zaben Shugaba Buhari Festus Keyamo ya ce wadanda suka yi taron da sunan kungiyoyin kabilun ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne da suka nuna goyon baya ga dan takararsu.