Da Dumi Dumi

Kungiyoyin mata sun yi addu’o’i domin mika mulki lami lafiya a Bauchi

Qungiyoyin mata a Bauchi

Hadakar kungiyoyin mata masu neman wanzuwar kare dimokaradiyya da cin moriyar dimokaradiyya da zama Lafiya a Jihar Bauchi sun gudanar da addu’o’i na musamman domin neman a mika mulki lami Lafiya ranan 29 ga watan Mayu mai zuwa a Jihar Bauchi

Taron addu’o’in wanda kungiyoyin suka yi shi a Masallacin Idi na kasuwar shanu  dake Bauchi, Matan sun yi kira wa Gwamnan mai barin gado da yabi tafarki na mutunci da mutuntawa domin a mika mulki cikin lumana kamar yadda aka yi zabubbuka lami Lafiya.

Jagorar matan Hajiya Addaji Muhammad ta ce makasudin kiran wannan gangami na yin addu’o’i shi ne abubuwa da suke faruwa, tun lokacin zabe har zuwa bayan zabubbuka a Jihar Bauchi abubuwane da ke iya jawo rudani da rashin zama lafiya, kuma duk lokacin da aka samu wani hatsaniya mata da yara sune suka fi shan wahala cikin lamarin.

Addaji ta ce “tun da doka ake bi a Najeriya dukkan madafun iko doka ne ya kafa su, bai kamata a yi kokarin wargaza abin da doka ta kafa ba, kuma ba daidai ba ne a ce shugabanni ne, suke koya wa magoya bayansu karya doka ba, don haka kowa ya sani ranar 29 ga watan Mayu da ke ciki ita ce ranar da za a rantsar da sabon Gwamnan da jama’ar Jihar Bauchi, suka zaba, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir Kauran Bauchi a matsayin Gwamna wannan shi ne abin da dokar kasa tace “

“Ta kara da cewa idan mutane zasu iya tunawa ana ta yawo da maganganu, da yawa da nufin kawo rudani a cikin jihar Bauchi. Tace lokacin da Gwamna mai barin gado ya sauya shawara ce wa zai Kalubalanci sakamakon zaben a kotu, sai ga fitattun mutane cikin magoya bayan sa sun shiga kafofin yada labarai suna baza jita jitar cewa ran 29 ga watan Mayu, Mohammed Abubakar za a rantsar.haka kuma aka kitsa cewa za a kama zababben Gwamna a rufeshi, sai bayan ranan rantsuwar ta wuce, a kai shi kotu a Abuja. Allah yasa Alkalin bai zauna ba, kwatsam yanzu kuma yan kwanaki ya rage a yi rantsuwar, sai gashi suna baza Jita Jitar cewa Gwamna mai barin gado zai mika mulki ga hannun babban Mai sharia na Jahar, ba zai ba wa zababben Gwamna ba, saboda an daga rantsuwa sai ranar 12 ga watan Yuni, duk kan waDannan batutuwa na neman kawo tashin hankali a jahar a cewar ta.”

ADVERTISEMENT

Addaji ta ce shi ya sa suka shirya gangamin adduo’i domin neman a zauna Lafiya a sami kwanciyar hankali, don zama lafiyar Jahar Bauchi, shine mafi alheri a garemu.

Jagorar matan ta roki hukumomin tsaro da su sa ido sosai kan dukkan wadansu masu yada Jita Jita da nufin jawo matsala wajen rantsar da sabon zababben Gwamnan Jahar Bauchi, da su gargadesu su yi hattara.

Kungiyar sun kuma nuna damuwa kan kwangiloli da Gwamnati mai barin gado ke ta bayarwa na biliyoyin nairori da kuma zargin daukar ma’aikata sama da dubu takwas, 8000 cikin yan kwanaki kafin mika mulki, da rabe raben filaye da motoci da cewa wannan ba abu ne da ya da ce ba, tunda tun cikin shekaru hudu da aka zabi Gwamnatin basu, yarda sun yi wadannan ayyukan ba, sai yan makonni kafin Gwamnatin ta kare.

Ta yi kira Gwamna mai jiran gado da cewa idan ya hau mulki, ya duba dukan wasu ayyuka da Gwamnati mai barin gado ta bayar da nufin samun ingantaccen gyara da bayar da su ta hanyar da ta fi dacewa ta amfani al’ummar Jihar Bauchi.

Share