✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyoyin tsaro na shiyya-shiyya ba za su haifar wa kasar nan alheri ba – Dokta Suleiman

Dokta Ahmed Jibrin Suleiman malami ne a Sashen Karatun Lauya da ke Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. A tattaunawarsa da Aminiya, ya ce kirkiro kungiyoyin tsaro…

Dokta Ahmed Jibrin Suleiman malami ne a Sashen Karatun Lauya da ke Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. A tattaunawarsa da Aminiya, ya ce kirkiro kungiyoyin tsaro na shiyya-shiyya a kasar nan ba zai haifar da da mai ido ba:

 

Kasancewarka malami a jami’a a bangaren shari’a, yaya kake hangen Najeriya za ta tunkari sauyin mulki a shekarar 2023 musamman ta fuskar tsaro?

Akwai batutuwa da dama da suke tasowa wadanda ba boyayyu ba ne kamar matsalar Boko Haram da masu garkuwa da mutane da rikicin makiyaya da manoma, dukkan wadannan matsaloli za a iya danganta su da harkar siyasa ta 2023.

A batun gaskiya wadannan matsaloli za a iya alkanta su da shirye-shiryen zaben shekarar 2023, amma babban abin bukata a yanzu shi ne Najeriya na bukatar ci gaba mai amfani da zaman lafiya mai dorewa fiye da tunanin zaben shekarar 2023.

Wani babban lamari da Najeriya ta samu kanta a ciki shi ne kimanin shekara goma da suka wuce an bar harkar tsaro ya lalace kuma  an yi  watsi da tsarin tsaro kasa, amma cikin yardar Allah zuwan Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015 ya maida da martabar da aka san tsaro da shi tare da karfafa musu gwiwa inda har aka fatattaki ’yan Boko Haram daga kananan hukumomin da suka kama a Jihar Barno.

Wani babban muhimmim mataki da Shugaba Buhari ya dauka shi ne na sake fasalin gudanar da harkar tsaro a Najeriya inda ya ce, harkar tsaro za ta tashi daga bangaran masu mulki kawai zuwa ga na daukacin ’yan Najeriya wanda tuni muka yi ta fafutikar ganin an ba al’umma damar sanya ido a harkar yadda ake tafiyar da tsaro a kasarmu. Kamar yadda ’yan siyasa suke shirya wa 2023 ko shakka babu za su yi iya yin duk mai yiwuwa domin yin barazana ga harkar tsaro ta yadda za ta yi daidai da bukatunsu.

Jihohin Kudu maso Yamma sun kafa Amotekun a matsayin ta tsaron yankinsu, kana ganin haka ba zai haifar da matsala ba ga fannin tsaro musamman yadda halin tsaro ke fuskantar barazana a yanzu?

A gaskiya mu kungiyoyi masu zaman kansu muna nuna damuwa sosai a kan barin yankuna su kafa jami’an tsaronsu, koda yake hadin gwiwa tsakanin al’umma da jami’an tsaro don samar da tsaro na da kyau matuka, amma hakan bai dace ba domin sauran yankunan Najeriya su ma za su kafa nasu wannan ba zai yi wa Najeriya kyau ba a matsayinta na kasa daya.

Babbar matsalar da rundunar Amotekun ke da shi kasancewar wani bangare guda ne na addini ya kafa kungiyar tsaron wanda hakan ya kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar jihohin Yarbawa, kamar Jihar Osun da wasu kungiyoyin addinai.

Wani abin lura kuma game da kungiyar tsaro ta Amotekun ba addinin kadai ba ne, akwai kabilanci da bangaranci tare da nuna kiyayya ga wani jinsi, wannan bai kamata ba domin sauran al’ummomi za su kafa nasu ta haka kuma komai na iya faruwa.

Abu na biyu shi ne in ka kalli yadda ake neman yi wa tsaron kasa karan-tsaye, wannan na nuni da cewa irin wadannan kungiyoyi na iya rikidewa su zama kungiyoyi tayar da zaune-tsaye ko na ’yan ta’adda a cikin al’umma.

A watannin baya daya daga cikin magabatan kasar nan Janar T Y Danjuma ya rika furta kalamai a Jami’ar Jihar Taraba da kuma garin Ibadan masu zafi a kan tsaron kasar nan, yaya kake ganin batunsa?

Ai kalamansa sun kasance abin mamaki da kunya domin yadda ’yan Najeriya ke matukar girmama shi da ba shi muhimmanci sai kawai ya fara sambatu ko soki-burutsu marasa kan gado. Wallahi mu dai a matsayinmu na malamai muna tir kuma muna nesanta kanmu da duk wanda ke neman wargaza hadin kan Najeriya bisa dalilin son zuciya.

Ya kamata al’ummar Najeriya musamman talakawa su yi hattara da mutane irin su Janar T.Y. Danjuma saboda in Najeriya ta yamutse za su kwashe iyalansu zuwa wata kasa don ci gaba da rayuwarsu ba tare da wata matsala ba. Shi kuwa talaka, sai yadda Allah Ya yi da shi domin ba ya da wani wurin zuwa.Ire-irin wadannan kalamai shi ma tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya rika yi musamman rubuta wasika ga shugabannnin kasa irin su Umaru Musa ’Yar’aduwa da Goodluck Jonathan da kuma Shugaba Buhari wadanda kuma duka ba su yi tasiri ba domin son zuciya ya dabaibaye wasikun nasa, amma ya manta cewa shi ma ya yi abin da ya gadama ba wanda ya ce da shi uffan.

To meee ce shawararka a karshe?

To shawara ga ’yan uwana ’yan Najeriya mu sa kasarmu ta zama abin alfahari a koyaushe, mu rika kishin kasarmu da al’ummarmu. Mu rungumi duk wani abin da zai kai mu ga ci gaban kasarmu da kanmu.