Search
Subscribe
‘Kura da Dila’

‘Kura da Dila’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatar alheri. A yau na kawo muku labarin ‘Kura da Dila’. Labarin ya kunshi yadda wayo ke fid da mutum daga matsala. A sha karatu lafiya:

 

Akwai wata kura wadda tsufa ya kama ta. Ga shi tana cikin jin yunwa ta rasa abin da yake mata dadi. Sai ta ce bari ta fita ko za ta ga ’yan uwanta. Tana fita sai ta ga babu ko daya a waje. Don haka sai ta ce bari ta fita neman abinci. Tana cikin tafiya, sai ta ga wani kokgo sai ta shiga. Ashe kogon na dila ne amma ya fita kiwo.

Dila na dawowa sai ya ji kogon shiru kuma ya san da cewa akwai tsuntsaye da sukan yi shawaginsu a ciki amma sai ya ji tsit. Kawai sai ya yi wata dabara ya ce, “Ya kai kogo! Yaya yau na ji ka tsit ne, bayan kuma kullum in na dawo kakan yi mini sannu da zuwa?”

Kura na jin haka sai ta budi baki ta ce “Sannu da zuwa abokina!”

Muryarta  ta sanya tsuntsayen suka fito a guje. Dila kuma na jin wannan murya da kuma yadda tsuntsayen suka razana, shi ma sai ya arce ya ce kafa me na ci ban baki ba. Kura da ta ji shiru sai ta gane cewa ashe dila ya yi mata wayo  ne.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin