✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurar da ta tashi bayan tube Sarki Sanusi II

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Kano ta tube Mai matraba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano bayan shafe…

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Kano ta tube Mai matraba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano bayan shafe kusan shekara uku ana sa-toka-sa-katsi a tsakanin bangarorin biyu, inda gwamnatin ta zarge shi da rashin biyayya ga ofishin Gwamnan Jihar da sauran hukumomin jihar.

Sai dai tube Sarki Sanusi ta tayar da kura  inda kasar ta dauki dumi, musamman yanayin yadda aka fitar da shi daga gidan sarauta da kuma kauye na farko da aka kai shi  wato Loko da ke Jihar Nasarawa a can gabar Kogin Benuwai.

Da yake bayar da sanarwar tube Sarkin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce Majalisar Zartarwar Jihar ce bisa jagorancin GwamnaAbdullahi Umar Ganduje ta tube Sarki Muhammadu Sanusi II daga sarauta saboda abin da ya aikata ya saba da sashi na 13 A zuwa E na Kundin Dokokin Masarautar Kano.

A cewarsa “Sarkin Kano ya nuna rashin biyayya ga Gwamnan Kano da kuma kin bin dokokin jihar. Hakan ya jawo gwamnati ta dauki matakin tube shi bayan ta tattauna da masu ruwa-da-tsaki.”

Tun a ranar Lahadin da ta gabata aka fara rade-radin za a tube Sarkin sakamakon girke jami’an tsaro a fadar Sarkin da wasu sassan birnin jda aka yi.

Majalisar Jihar Kano ta hautsine kan yukurin tsigewar

A safiyar Litinin an samu kai-ruwa-rana a tsakanin mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano kan rigimar da ke tsakanin Gwamnatin Kano da kuma tsohon Sarkin Kano.

Rigimar ta fara ce bayan da Shugaban Kwamitin Sauraren Korafe-korafen Jama’a na Majalisar Alhaji Hamza Rabi’u Masu ya yi bayanin game da hanzarinsa kan korafe-korafe biyu da aka yi a kan Sarkin wanda  aka ba kwamitinsa aikin bincikawa. Hakan ya jawo wadansu mambobin majalisar  daga Jam’iyyar PDP suka kalubalance shi cewa abin da ya yi ya saba da dokar majalisar cewa idan majalisar tana zama ba a yin magana a kan wani korafi da ke gaban wani kwamiti da bai mika rahotonsa ga majalisar ba.

Hakan ya jawo mambobin majalisar na jam’iyyun APC da PDP suka fara fada da juna inda suka yi yunkurin karya sandar majalisar kafin a karshe jami’an tsaro su yi nasarar dauke sandar.

Yadda lamarin ya samo asali

Idan za a iya tunawa dai tun bayan da aka kammala zaben bara aka fara samun rikici tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Sarkin Kano inda gwamnatin ta kai ga kirkiro sababbin masarautu hudu daga Masarautar Kano. Haka kuma gwamnatin ta hannun Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta fara tuhumar Sarkin game da wasu kudade mallakar masarautar da ake zarin ya yi almubazzarancin da su.

A makon jiya kuma sai Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara bincike a kan wani korafi da wata kungiya ta yi cewa ana zargin Sarkin da yi wa al’adun Jihar Kano karan-tsaye. Ana cikin hakan kuma sai wancan hukuma ta sake gayyatar Sarkin ya bayyana a gabanta don amsa wasu tuhume-tuhume a kan wasu filaye na Gandun Sarki da gwamnatin ta zarge shi da sayarwa. Hakan ya sa Sarkin ya garzaya kotu inda ta dakatar da wancan bincike da ta fara yi wa Sarki har sai an saurari korafin da ya shigar gaban kotun.

Tarihi ya maimaita kansa

Tube Sarki Sanusi II da Gwamnatin Jihar Kano ta yi abu ne da tarihi ya maimaiata kansa lura da cewa ya gaji kakansa a cikin jerin sarakunan Kano ne wadanda suka saba mutuwa a kan karagar mulki. A 1963 Gwamnatin Arewa ta sauke kakansa, Sarki Muhammadu Sanusi I.

’Ya’yan marigayi Sarki Ado Bayero sun zama sarakunan Kano da Bichi

A yamamcin ranar da aka tube Sarki Sanusi II, Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da sanarwar nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano wanda aka yi a gaban masu nadin Sarki na Masarautar Kano da suka hada da Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabhani da Makman Kano Alhaji Ibrahim Makama da Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtari Adnan da Sarkin Dawaki Maituta Alhaji Bello Tuta.

Kafin nada shi Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Bichi daya daga cikin sababbin masarautun da gwamnatin ta kirkiro bara. Haka kuma gwamnmatin ta nada Alhaji Nasiru Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Bichi. Kafin nadin nasa shi ne Chiroman Kano kuma Hakimin Nasarawa.

Ra’ayin al’ummar Kano

Aminiya ta ji ra’ayin al’ummar Jihar Kano game da batun tube Sarkin, inda mafi yawan jama’a suka fi nuna tausayawarsu ga tubababen Sarkin yayin da wadansu ke murna da nadin sabon Sarkin.

Farfesa Tijjani Naniya, Malami a Sashin Tarihi na Jami’ar Bayero ya  ce tube Sarkin da Gwamnatin Jihar Kano ta yi ba ya bisa ka’ida kasancewar hujjojin da gwamnatin ta bayar ba su da karfin da har za a iya sauke Sarkin. A cewar Tijjani Naniya abin da Gwamnatin Jihar Kano ta yi abu ne da zai zubar da mutunci da darajar masarautar “Shi ke nan idan aka sake samun wata gwamnati ita ma ta ga ba ta ra’ayin Sarki sai ta tube shi. Kin ga shi ke nan wayi gari an rasa tarihi da al’ada. Duk kuma al’ummar da ta rasa wadannan abubuwa biyu to tana cikin garari.”   Ya ce haka kuma gwamnatin ba ta bi tsarin tafiyar da gwamnati kafin ta tube Sarkin ba.

Wani dan kasuwa Malam Aminu Alkassim, ya nuna rashin jin dadinsa game da abin da ya faru inda ya ce matakin da Gwamnatin Kano ta dauka ya kara lllata harkar Masarautar Kano, lura da cewa ana kokarin y siyasantar da masarauta. “Babban abin bakin ciki a wannan lamari shi ne yadda ake kokarin siyasantar da Masarautar Kano. Zai kasance idan aka yi sabon Gwamna to shi ma zai yi nasa Sarkin.”

Ra’ayin al’ummar Kano

Wani matashi Ash’ari ya bayyana lamarin a matsayin hukuncin Allah, amma ba laifin Gwamnatin Jihar Kano ba, domin a cewarsa komai na duniya lokaci gare shi, “Allah Ya kadarta cewa lokacin Sarki Sanusi na mulkin Kano ya kare, kuma har wani ya hau, Don haka ban ga wani abu na jin haushi ba. Muna murna da wannan sabon Sarki da aka yi,” inji shi.

Sumayya Rabi’u kuwa cewa ta yi abin da Gwamnatin Kano ta yi ta yi shi ne don ramuwar gayya don haka wannan abin kunya ne ga gwamnatin. “Yaya za a ce shugaba zai zama mai kullata da rashin yafiya? Idan har Sarki bai goyi bayansa a siyasa ba to shi ba zai yafe masa a zo a yi tafiya tare ba? Kuma ma shi Sarki ba mutum ba ne, shi ba shi da ra’ayin siyasa?”

Malam Ali Sanusi a nasa ra’ayin ya  ce abin da ya faru ga Sarki Sanusi abu ne da zai zame masa daukaka a nan gaba, “Babu abin da zai faru da Sarki sai alheri,  domin hassada ga mai rabo taki ce. Shi Sarki kadara ce ba kawai ga Kano ba har da Najeriya. Nan ba da dadewa ba makiyansa za su yi tagumi a kan abin da Allah zai yi masa na daukaka,” inji shi.

Wadansu iyalansa sun koma Legas

Aminiya ta jiyo cewa tun a ranar Litinin aka fara kwashe kayayyakin iyalan tsohon Sarkin har zuwa ranar Talata. “Da yake dama wadansu daga cikin matansa ba sa gari, to su biyun da suka rage bayan sun raka shi filin jirgi daga nan aka kwashe su da ’ya’yansu da suka rage domin mafi yawan ’ya’yan suna makaranta, aka kai su Jihar Legas,” inji wata majiyar iyalansa.

Mahaifiyar tubabben Sarkin Hajiya Mai Babban Daki tuni ta bar gidan da take zaune na Sarautar Mai Babban Daki da ke Unguwar Gwangwazo.

Hakimai sun yi mubaya’a ga Sabon Sarki

A ranar Talata ce sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyara kabarin mahaifinsa marigayi Alhaji Ado Bayero da ke gidan Sarki na Nassarawa don yin addu’a gare shi.

Sarki Aminu Ado cikin rakiyar wadansu daga cikin hakimansa da suka hada da Turakin Kano da Talban Kano da Dan Darman Kano ya isa kabarin da misalin karfe 12 na rana.

Sarki Aminu Ado da hakimansa sun gudanar da addu’o’i ga mahaifinsa daga nan  ya zauna a fadar da ke gidan inda hakiman suka rika shigowa suna masa mubaya’a. Daga cikin hakiman da aka ga fuskokinsu sun hada da Hakimin Fagge da na Dala da kuma wadansu da ke rike da saurautun gargajiya da suka hada da Talban Kano da Turakin Kano da masu nadin Sarki su hudu da sauransu.

Daga nan sabon Sarkin ya kai ziyara gidan mahaifiyarsa da ke Unguwar Gadun Albasa a wani mataki na neman albarkarta inda ita da sauran iyalan marigayi Sarki Ado Bayero suka karbe shi tare da yi masa addu’o’in samun nasara.

Jami’an tsaro na hana sarakunan Nasarawa ganin tsohon Sarkin Kano

Jami’am tsaro da aka girke don tsaron tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II sun hana wadansu sarakuna da sauran manyan mutane ganawa da shi a farkon zuwansa.

A shekaranjiya Laraba an hana Sarkin Karshi da Sarkin Uke da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa da suka je don su gana da shi.

Sarkin Karshi Dokta Muhammad Sani Bako da Sarkin Uke, Alhaji Ahmad Abdullahi sun kwashe kimanin kilomita 250 don zuwa garin Awe, inda suka isa gidan Sarkin Awe, Alhaji Isa Abubakar Umar II inda suka gana shi da karfe 1:00 na rana.

Daga nan sai suka nufi gidan da ake ajiye  tsohon Sarkin Kano da kimanin karfe 1:30 na rana, amma sai wani dan sanda mai suna ASP Esson ya tubure cewa kada a yi fushi da shi, domin su suna aiki ne da umarni da aka ba su daga manyansu.

Ana cikin haka suka ce ba sa son su ga ’yan jarida a wajen. Kuma bayan kamar minti biyar, sai sarakunan suka juya suka koma gidan Sarkin Awe, sannan da misalin kare 2:00 na rana suka koma masarautunsu.

Garin Awe da aka kai Sarki Sanusi  II

Uban-Garin Awe, Alhaji Muhammadu Adam Sa’idu, ya ce, garin Awe na da tsohon tarihi, inda ya ce an kafa garin ne kimamin shekara 300 da suka wuce. “Katsinawa daga garin ’Yan Tumaki ne suke mulkin garin. Kuma sunan ya samo asali daga harshen Jukun a harshen Jukun Awi na nufin wurin da ake samum namun daji, daga bisani ne ya rikide zuwa Awe,” inji shi.

Ya ce “Sarkin Awe na yanzu, Alhaji Isa Abubakar Umar II, shi ne Sarkin na 16.”

“Manyan sana’o’in mutanen garin su ne noma da hakar gishiri wanda kuma har yanzu suna yin wannan sana’a,” inji Uban Garn Awe.

Aminiya ta gano garin Awe yana da kabilun da suka hada da Hausawa da Fulani da Jukun da Angyarawa da Gwandara da Arago da sauransu. Akwai makarantu biyar a garin,  firamare  3 da  karamar  sakandare daya da babbar sakandare daya, sai dai babu ruwan famfo a garin, amma akwai masu sayen ruwa su sayar daga rijiyoyin burtsatse.Bugu da kari, ana samun wutar lantarki a kwana daya, a dauke ta kwana daya, sannan ana sanum na kimanin awa 20 a rana.

Daga Lafiya, Hedikwatar Jihar Nasarawa zuwa garin Awe kilomita 90 ne, kuma toshon Gwamnan Jihar Sanata Umaru Al-Makura ne ya gina musu hanya mai kyau.

Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Umar Dan-Akano ya shaida wa Aminiya cewa ba zai yi magana kan lamarin ba.

Wani magidanci, mai suna Ibrahim Usman Fulani  ya ce, “Tube tsohon Sarkin Kano Sanusi II da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi, ya yi mana zafi, amma kuma kaddara ce. Muna kuma murna da kawo mana shi garinmu. Ni ba inda za ni har sai na zo na yi masa rakiya ranar Juma’a, don in gan shi inji dadi.”

Gidan da aka ajiye shi

Magatakardar Majalisar Karamar Hukumar Awe, kuma wata daga cikin masu yi wa masu tsaron Sarkin hidima, Hajiya Fatima Kande Umar ta ce, “Gidan da aka ajiye tsohon Sarki yana da bangarori uku, bangaren maigidan da bangarori biyu na mata, kuma kowane na da falo da bangaren cin abinci da ban-daki da wajen dafa abinci.”

Aminiya ta lura cewa a gidan akwai na’urorin sanyaya daki na zamani da rijiyar burtsatse, akwai kuma wata mota baka a ciki. Sannan gidan na zagaye ne da gidajen talakawa, kuma akwai matasa zaune a masallacin kofar gidan.

Iyalan Sarki Sanusi sun isa Awe

Shekaranjiya Laraba da misalin karfe 11:00 na rana, daya daga cikin matan tsohon Sarkin da wadansu daga cikin ’ya’yansa suka isa gidan a cikin wata farar mota kirar Jeep Infiniti tare da rakiyar motocin Gwamnatin Jihar Kaduna kira Toyota Hilud da daya ke da lamba 02L 03KD.  Kuma da misalin karfe 12:00 aka kunna janareta a gidan, saboda a ranar ce ake sa ran za a kawo wutar lantarki, amma ba a kawo ba, har zuwa karfe uku na rana.

Daga bisani Sarkin Awe da Sarkin Azara sun shiga suka gana da shi. Amma daga baya al’amari ya sauya, inda ’yan sanda suka ce ba za su yarda a kara ganinsa ba saboda umarni  aka ba su.

An ce garin na Awe yana da akalla mutum dubu 200.

Gwamnan Kaduna ya ba Sanusi mukamai biyu

Awoyi kadan bayan tube Sarkin ne, sai Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanar da nada shi a matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar Bunkasa Zuba Jari da Kasuwanci ta Jihar Kaduna (KADIPA).

Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Muyewa Adekeye  ta ce mutum mai ilimi irin Muhammadu Sanusi ll bai kamata a bar shi haka ba.

Ya ce nadin ya biyo bayan garambawul ga shugabannin Hukumar KADIPA da Mataimakiyar Gwamna ke jagoranta. Tuni wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa tsohon Sarkin ya karbi mukamin.

A shekaranjiya Laraba kuma, Gwamnan ya sake nada tsohon Sarkin a matsayin Uban Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), inda zai maye gurbin Sarkin Moro’a Malam Tagwai Sambo wanda ya rike matsayin na farko.

Akwai kyakkyawar dangantaka a tsakanin Malam Sanusi II da Gwamna El-Rufa’i wadanda bayan kasancewarsu ’yan boko masu ra’ayin sauyi, bayanai sun ce lokacin da Malam Sanusi II ke Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya taba ba wani kamfanin Gwaman El-Rufa’i wata kwangila mai tsoka.

Wannan kyakkyawar dangata  ce ta sa tsohon Sarkin ke halartar duk wani biki ko hidima da Gwamna El-Rufa’i ya gayyace shi, kuma wadansu na ganin kalaman da tsohon Sarkin ya yi wajen bikin cikar Gwamna El-Rufa’i shekara 60, sun dada  tunzura Gwamna Ganduje kuma ana ji suna daga cikin abubuwan da suka sanya shi tube Sarkin.

Kuma a jiya Alhamis Aminiya ta samu labarin cewa Gwamna El-Rufa’i ya tafi garin Awe da ke Jihar Nasarawa inda ya gana da tsohon Sarkin. Wata majiya ta ce, daga Kaduna Gwamnan ya je Awe, amma duk kokarin da Aminiya ta yi don ta tabbatar da haka daga Kakakin Gwamnan Malam Ibrahim Musa ya ci tura, saboda wayoyinsa suna rufe a daidai lokacin. Idan haka ta tabbata zai kasance aminin Sarkin na farko kuma Gwamna na farko da ya ziyarci tsohon Sarkin tun bayan tube shi.

Mun kafa tarihi a Kano-Ganduje

A yammacin shekaranjiya Laraba ce Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya mika takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma takwaransa na Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Dubban mutane da suka hada da masu rike da sarautun gargajiya na Masarsutar Kano da Bichi da sauran masarautu uku da ke jihar da mukarraban Gwamnatin Jihar da sauran jama’ar birni ne suka halarci kasaitaccen bikin mika takardar fara aikin wanda aka yi a Fadar Gwamnatin Jihar.

Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce bikin ya kafa tarihi a jihar wanda ba a taba yi ba game da yadda aka nada sarakuna biyu wadanda suke ’yan uwan juna ne a lokaci guda.

A jawabansu daban-daban sarakunan sun nuna godiyarsu ga Allah (SWT) bisa sarautun da suka samu inda suka nemi hadin kan alummar Jihar Kano .

Wane ne Sarki Aminu Ado Bayero?

An haifi Alhaji Aminu Bayero a birnin Kano ranar 21 ga Agusta, 1961, gabanin mahaifinsa Ado Bayero ya zama Sarkin Kano da shekara biyu.