✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurar da ta tashi bayan tube Sarki Sanusi II

Yadda Sanusi II ke rayuwa a Awe Ba hannuna a tube shi – Buhari A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Kano ta…

  • Yadda Sanusi II ke rayuwa a Awe
  • Ba hannuna a tube shi – Buhari

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Kano ta tube Mai matraba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano bayan shafe kusan shekara uku ana sa-toka-sa-katsi a tsakanin bangarorin biyu, inda gwamnatin ta zarge shi da rashin biyayya ga ofishin Gwamnan Jihar da sauran hukumomin jihar.

Sai dai tube Sarki Sanusi ta tayar da kura  inda kasar ta dauki dumi, musamman yanayin yadda aka fitar da shi daga gidan sarauta da kuma kauye na farko da aka kai shi  wato Loko da ke Jihar Nasarawa a can gabar Kogin Benuwai.

Da yake bayar da sanarwar tube Sarkin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ya ce Majalisar Zartarwar Jihar ce bisa jagorancin GwamnaAbdullahi Umar Ganduje ta tube Sarki Muhammadu Sanusi II daga sarauta saboda abin da ya aikata ya saba da sashi na 13 A zuwa E na Kundin Dokokin Masarautar Kano.

A cewarsa “Sarkin Kano ya nuna rashin biyayya ga Gwamnan Kano da kuma kin bin dokokin jihar. Hakan ya jawo gwamnati ta dauki matakin tube shi bayan ta tattauna da masu ruwa-da-tsaki.”

Tun a ranar Lahadin da ta gabata aka fara rade-radin za a tube Sarkin sakamakon girke jami’an tsaro a fadar Sarkin da wasu sassan birnin jda aka yi.

Majalisar Jihar Kano ta hautsine kan yukurin tsigewar

A safiyar Litinin an samu kai-ruwa-rana a tsakanin mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano kan rigimar da ke tsakanin Gwamnatin Kano da kuma tsohon Sarkin Kano.

Rigimar ta fara ce bayan da Shugaban Kwamitin Sauraren Korafe-korafen Jama’a na Majalisar Alhaji Hamza Rabi’u Masu ya yi bayanin game da hanzarinsa kan korafe-korafe biyu da aka yi a kan Sarkin wanda  aka ba kwamitinsa aikin bincikawa. Hakan ya jawo wadansu mambobin majalisar  daga Jam’iyyar PDP suka kalubalance shi cewa abin da ya yi ya saba da dokar majalisar cewa idan majalisar tana zama ba a yin magana a kan wani korafi da ke gaban wani kwamiti da bai mika rahotonsa ga majalisar ba.

Hakan ya jawo mambobin majalisar na jam’iyyun APC da PDP suka fara fada da juna inda suka yi yunkurin karya sandar majalisar kafin a karshe jami’an tsaro su yi nasarar dauke sandar.

Yadda lamarin ya samo asali

Idan za a iya tunawa dai tun bayan da aka kammala zaben bara aka fara samun rikici tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Sarkin Kano inda gwamnatin ta kai ga kirkiro sababbin masarautu hudu daga Masarautar Kano. Haka kuma gwamnatin ta hannun Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta fara tuhumar Sarkin game da wasu kudade mallakar masarautar da ake zarin ya yi almubazzarancin da su.

A makon jiya kuma sai Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara bincike a kan wani korafi da wata kungiya ta yi cewa ana zargin Sarkin da yi wa al’adun Jihar Kano karan-tsaye. Ana cikin hakan kuma sai wancan hukuma ta sake gayyatar Sarkin ya bayyana a gabanta don amsa wasu tuhume-tuhume a kan wasu filaye na Gandun Sarki da gwamnatin ta zarge shi da sayarwa. Hakan ya sa Sarkin ya garzaya kotu inda ta dakatar da wancan bincike da ta fara yi wa Sarki har sai an saurari korafin da ya shigar gaban kotun.

Tarihi ya maimaita kansa

Tube Sarki Sanusi II da Gwamnatin Jihar Kano ta yi abu ne da tarihi ya maimaiata kansa lura da cewa ya gaji kakansa a cikin jerin sarakunan Kano ne wadanda suka saba mutuwa a kan karagar mulki. A 1963 Gwamnatin Arewa ta sauke kakansa, Sarki Muhammadu Sanusi I.

’Ya’yan marigayi Sarki Ado Bayero sun zama sarakunan Kano da Bichi

A yamamcin ranar da aka tube Sarki Sanusi II, Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da sanarwar nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano wanda aka yi a gaban masu nadin Sarki na Masarautar Kano da suka hada da Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabhani da Makman Kano Alhaji Ibrahim Makama da Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtari Adnan da Sarkin Dawaki Maituta Alhaji Bello Tuta.

Kafin nada shi Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Bichi daya daga cikin sababbin masarautun da gwamnatin ta kirkiro bara. Haka kuma gwamnmatin ta nada Alhaji Nasiru Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Bichi. Kafin nadin nasa shi ne Chiroman Kano kuma Hakimin Nasarawa.

Ra’ayin al’ummar Kano

Aminiya ta ji ra’ayin al’ummar Jihar Kano game da batun tube Sarkin, inda mafi yawan jama’a suka fi nuna tausayawarsu ga tubababen Sarkin yayin da wadansu ke murna da nadin sabon Sarkin.

Farfesa Tijjani Naniya, Malami a Sashin Tarihi na Jami’ar Bayero ya  ce tube Sarkin da Gwamnatin Jihar Kano ta yi ba ya bisa ka’ida kasancewar hujjojin da gwamnatin ta bayar ba su da karfin da har za a iya sauke Sarkin. A cewar Tijjani Naniya abin da Gwamnatin Jihar Kano ta yi abu ne da zai zubar da mutunci da darajar masarautar “Shi ke nan idan aka sake samun wata gwamnati ita ma ta ga ba ta ra’ayin Sarki sai ta tube shi. Kin ga shi ke nan wayi gari an rasa tarihi da al’ada. Duk kuma al’ummar da ta rasa wadannan abubuwa biyu to tana cikin garari.”   Ya ce haka kuma gwamnatin ba ta bi tsarin tafiyar da gwamnati kafin ta tube Sarkin ba.

Wani dan kasuwa Malam Aminu Alkassim, ya nuna rashin jin dadinsa game da abin da ya faru inda ya ce matakin da Gwamnatin Kano ta dauka ya kara lllata harkar Masarautar Kano, lura da cewa ana kokarin y siyasantar da masarauta. “Babban abin bakin ciki a wannan lamari shi ne yadda ake kokarin siyasantar da Masarautar Kano. Zai kasance idan aka yi sabon Gwamna to shi ma zai yi nasa Sarkin.”

Wani matashi Ash’ari ya bayyana lamarin a matsayin hukuncin Allah, amma ba laifin Gwamnatin Jihar Kano ba, domin a cewarsa komai na duniya lokaci gare shi, “Allah Ya kadarta cewa lokacin Sarki Sanusi na mulkin Kano ya kare, kuma har wani ya hau, Don haka ban ga wani abu na jin haushi ba. Muna murna da wannan sabon Sarki da aka yi,” inji shi.

Sumayya Rabi’u kuwa cewa ta yi abin da Gwamnatin Kano ta yi ta yi shi ne don ramuwar gayya don haka wannan abin kunya ne ga gwamnatin. “Yaya za a ce shugaba zai zama mai kullata da rashin yafiya? Idan har Sarki bai goyi bayansa a siyasa ba to shi ba zai yafe masa a zo a yi tafiya tare ba? Kuma ma shi Sarki ba mutum ba ne, shi ba shi da ra’ayin siyasa?”

Malam Ali Sanusi a nasa ra’ayin ya  ce abin da ya faru ga Sarki Sanusi abu ne da zai zame masa daukaka a nan gaba, “Babu abin da zai faru da Sarki sai alheri,  domin hassada ga mai rabo taki ce. Shi Sarki kadara ce ba kawai ga Kano ba har da Najeriya. Nan ba da dadewa ba makiyansa za su yi tagumi a kan abin da Allah zai yi masa na daukaka,” inji shi.

Wadansu iyalansa sun koma Legas

Aminiya ta jiyo cewa tun a ranar Litinin aka fara kwashe kayayyakin iyalan tsohon Sarkin har zuwa ranar Talata. “Da yake A 1990 mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya fara ba shi sarauta, inda aka nada shi Dan Majen Kano kuma Hakimin Nasarawa.

Daga nan ne kuma aka kara masa girma zuwa Dan Majen Kano Hakimin Gwale a shekarar 1990.

A shekrar 1991 kuma likkafa ta kara gaba inda aka nada shi Turakin Kano kuma Hakimin Dala a watan Janairun 1991 zuwa Janairun 2001, ma’ana dai ya shekara 10 a wannan mukami.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Dala daga watan Janairun 2001sarautar da ya rike har zuwa 2014.

Daga nan ne kuma aka kara masa girma

A watan Oktoban 2014 Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nada shi  Wamban Kano kuma dan Majalisar Sarki. Ya rike sarautar har zuwa watan Mayun 2019.

A watan Disamban 2019 ne kuma Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi Sarkin Bichi na farko bayan kirkiro sababbin masarautu a jihar.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya fara karatu a makarantar firamare ta Kofar Kudu daga 1967 zuwa 1974.

Daga nan ne kuma ya tafi zuwa Kwalejin Gwamnati ta Birnin Kudu a Jihar Jigawa ta yanzu, inda ya yi karatun sakandare.

Alhaji Aminu Bayero ya halarci Jami’ar Bayero inda ya samu digiri a fannin Aikin Jarida da Kimiyyar Siyasa daga 1979 zuwa 1984.

Haka kuma ya yi aikin hidimar kasa a Jihar Binuwe inda ya yi aiki a Gidan Talabijin na Kasa (NTA).

Sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado ya fara aiki a Kamfanin Jiragen Sama na Kabo Air, a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a daga 1985 zuwa 1990 inda ya rike matsayin darakta a kamafanin.

A bangaren kungiyoyi kuwa, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne Shugaban Kungiyar Wasan Kwallon Kwando ta Jihar Kano, kuma shi ne Uban Kungiyar ’Yan Asalin Ilorin Mazauna Kano kamar yadda BBC ya kalato.

Buhari ne ya bayar da umarnin cire Sarki Sanusi – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya dora alhakin tube Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan Shugaba Muhammadu Buhari.

“Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin al’amuran Jihar Kano. Inda ya kamata ya sa hannun sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga a nan ya sa hannu,” inji Kwankwaso.

Kwankwaso, wanda a zamanin mulkinsa ne a shekarar 2014 aka nada Sarki Muhammadu Sanusi II, ya yi wannan kalami ne lokacin zantawarsa da BBC a kan batun tube tsohon Sarkin.

Ba ni da hannu a tube Sarki Sanusi II – Buhari

Sai dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba ya da hannu a tube tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ne ya wallafa haka a shafinsa na Tiwita a shekaranjiya Laraba, inda ya ce dukkan maganganun da ake yadawa ba gaskiya ba ne kuma siyasa ce.

Ya ce Shugaban Kasa bai taba katsalanda a cikin harkokin wata jiha a kasar nan ba sai dai idan hakan ya shafi tsaron kasar baki daya.

Malam Garba Shehu ya  ce, nada Sarki da kuma tube shi ya rataya ne a kan gwamnatocin jihohi ba na tarayya ba.

Ya ce ba adalci ba ne masu hamayya da gwamnati su rika kokarin alakanta abin da ya faru a Jihar Kano da Gwamnatin Tarayya.

Shugaban Kasar kuma ya yabi mutanen Kano kan dattakun da suka nuna na kin tayar-da-zauna tsaye bayan tube Sarki Sanusi, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Yadda aka cire Sarkin Kano na kama da mulkin kama-karya – Sheikh Dahiru Bauchi

Da yake karin haske kan batun, fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya sha nuna goyon baya ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi  II,ya ce  yadda aka tube Sarkin yana kama da mulkin kama-karya.

“Duk abin da mutane suke nufi ba abin da zai zartu sai wanda Allah Yake nufi. Ainihi Sarkin KanoMuhammadu Sunusi II ya gaji kakansa cikin samun Sarautar Kano kuma ya gaji kakansa a cikin fita dagacikin sarautar. Allah ne Ya shigar da shi sarautar, kuma Shi ne Ya karba, kuma wani lokacin in Ya so sai Ya mayar da shi kan sarautarsa. Allah Yana da ikon yin haka,” inji Shehin.

Shehin ya kara da cewa, “Abin da muke fata Allah Ya saka da alheri amma su wadanda suka yi wannan abu ba mu ji dadin abin da suka aikata ba, saboda ba mu da iko sai abin da Allah Ya yi, amma muna da addu’a. Allah Ya kiyaye Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Allah Ya ba shi alheri.”

A karshe ya ce, “Muna kira ga jama’ar Kano da kada a tada hankali, kada a ce za a yi zanga-zanga ko wani abu. Abin da za a yi shi ne addu’ar Allah Ya yi mana mafita, amma kada a dauki doka a hannu.”