✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurona: ’Yan kasuwar kayayyakin lantarki sun shiga tasku

’Yan Najeriya da suke tafiya kasar China sayo kayayyaki masu amfani da lantarki su kawo Najeriya su sayar, sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon annobar…

’Yan Najeriya da suke tafiya kasar China sayo kayayyaki masu amfani da lantarki su kawo Najeriya su sayar, sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon annobar cutar Kurona da ta fara bulla a kasar China  kuma take yaduwa a kasashe duniya.

Da yake zantawa da Aminiya kan batun, wani dan kasuwa da ke zuwa kasar China sayo kayayyakin wutar lantarki, Alhaji Sani Sulaiman Saminaka, ya ce ya kai shekara 12 yana zuwa kasar China sayo kayayyakin wutar lantarki, kuma duk shekara yana zuwa kamar sau uku.

Ya ce gaskiya su da suke zuwa China sayo kayayyakin lantarki, suna cikin mawuyacin hali, domin komai na harkokin kasuwancinsu ya yi kasa, saboda mutanen China da suke zuwa sarin kayayyaki a wurinsu duk sun  rufe masana’antu da harkokin kasuwanci kowa yana gida, saboda  annobar cutar Kurona.

“Zuwa yanzu kayayyakin kasar China, sun fara karanci a Najeriya. Saboda rashin ciniki ne, ya sanya kayayyakin ba su yi mugun tashi ba. Don haka mutane ba su gane kayayyakin sun fara wahala ba. Amma duk da haka wasu kayayyakin sun fara karanci, a kasuwannin Najeriya,’’ inji shi.

Ya ce idan wannan annoba ta ci gaba za a samu matsala a duniya baki daya. Don akwai yiwuwar za a iya rasa kayayyakin kasar China baki daya a kasashe da dama.

Ya ce kayayyakin lantarki na China da sauran kayayyakin da suke yi, sun karbu a duniya saboda araharsu da ingancinsu. Hakan ne ya sa duk duniya, babu inda ba sa amfani da kayayyakin kasar China.

Ya yi kira ga al’ummar duniya su koma ga Allah a ci gaba da addu’o’in Allah Ya kawo karshen wannan annoba, musamman ganin yadda ta yadu a duniya da kuma yadda ta shafi tattalin arzkin duniya.