Da Dumi Dumi

Kusancin Lalong ga Buhari ya yi wa Filato alfanu – Dan Manjang

Mista Dan Manjang

Mista Dan Manjang shi ne Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Filato, ya yi bayanai kan kusancin Gwamnan Jihar Simon Lalong, ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da irin alherin da wannan kusanci ya kawo wa jihar:

 

Mane ne dalilin da Gwamna Lalong yake yin kusa da Shugaban Kasa Buhari?

Idan Gwamna Lalong bai yi kusa da Shugaban Kasa Buhari ba, wane ne zai yi kusa da shi?  A Najeriya muna da Shugaban Kasa guda 2 ne?  Yanzu a Najeriya ba mu da wani Shugaban Kasa, sai Shugaba Buhari. Don haka Shugaban Kasa na kowa ne iri ne, ko daga wacce kabila yake, ko daga wane addini yake, ko daga wace jam’iyya yake Shugaban Najeriya ne. Don haka idan Gwamna ya san abin da yake yi, dole ne ya yi kusa da shi, domin ya samo wa al’ummarsa abubuwan da suka kamata su samu.

Kuma wannan kusanci na Gwamna Lalong da Shugaban Kasa Buhari, al’ummar Jihar Filato sun ga amfaninsa. Domin akwai abubuwa da yawa da aka yi wa Jihar Filato, sakamakon wannan kusanci na Gwamna Lalong ga Shugaban Kasa Buhari. Misali idan ka dubi sha’anin zaman lafiya a Jihar Filato, an yi barikin soja a Shendam da Gashishi. An kawo sojojin sama an ajiye a Kerang. Da Gwamna Lalong ba ya kusantar Shugaban Kasa, ba za a iya samun wadannan abubuwa ba.

ADVERTISEMENT

Ana rade-radin cewa Gwamna Lalong yana son ya tsaya takarar Mataimakin Shugaban Kasa, a zaben shekarar 2023, mece ce gaskiyar wannan magana?

Wane ne a Najeriya idan aka ba shi Mataimakin Shugaban Kasa zai ki? Saboda haka masu irin wadannan maganganu, suna shaci-fadi ne kawai. Kuma masu irin wadannan maganganu, sun rasa inda za su dafa ne. Idan aka bai wa Gwamna Lalong Shugaban Kasa ko Mataimakin Shugaban Kasa sai ya ki? Ai ba ana tsayawa takarar Mataimakin Shugaban Kasa ba ne. Wannan aiki ne na jam’iyya, idan jam’iyya ta ga cewa mutum ya cancanta, sai ta ce wannan mutumin ne zai tsaya mana takarar Mataimakin Shugaban Kasa, domin a tafi tare a tsira tare. Saboda haka idan al’ummar Najeriya suka ga cewa Gwamna Lalong, ya dace ya zama Mataimakin Shugaban Kasa, babu wata illa a ciki.

Amma yanzu babban abin da Gwamna Lalong ya sanya a gaba, shi ne sauke nauyin mulkin da al’ummar Jihar Filato suka dora masa ta hanyar zabensa. Don haka abin da Gwamna Lalong ya sanya a gaba shi ne raya Jihar Filato, domin idan wadanda za su gaje shi, suka zo kada su samu wata matsala kamar yadda aka samu a baya.

Me za ka ce kan koke-koken da wadansu ’yan jihar nan suke yi, kan yawan tafiye-tafiyen da Gwamna Lalong ke yi?

Idan Gwamna Lalong bai yi tafiya ba za a yi magana, idan ya yi tafiya za a yi magana, idan ya kwanta za a yi magana, idan ya kasa barci za a yi magana, duk abin da ka yi mutane sai sun yi magana.

Saboda haka Gwamna Lalong zai ci gaba da yin tafiye-tafiye idan ta dauro. Ba za mu guji tafiye-tafiye ba, domin wadannan tafiye-tafiye na Gwamna Lalong suna kawo wa Jihar Filato alherai daban-daban. Akwai ayyuka da dama da muka samu a Jihar Filato, ta dalilin irin wadannan tafiye tafiye. Misali idan ka dauki hanyar Keffi za a yi tagwayen hanya daga Keffi zuwa Akwanga zuwa Jos zuwa Gombe. Idan Gwamna Lalong ba ya tafiya, ya ya za a sami wannan abu?

Kwanan nan sakamakon wadannan tafiye-tafiyeN, gwamnati kasar Japan ta tallafa wa Jihar Filato da Dala miliyan 30. Mutanen Filato masu tunani sun ga amfanin tafiye-tafiyen Gwamna Lalong.

Me za ka ce a kan koken da Jam’iyyar PDP ta yi, kan matakin da Gwamna Lalong ya dauka, na rantsar da ’yan takarar kujerar shugabancin kananan hukumomi na Jam’iyyar APC, a matsayin shugabannin riko a kananan hukumomin da ba a yi zabe?

Ai ba ’yan takarar APC kadai aka rantsar ba, har da ’yan PDP aka rantsar. Shugaban Karamar Hukumar Langtang ta Arewa da aka rantsar tare da wadannan shugabannin kananan hukumomi na riko, ai dan PDP ne. A lokacin mulkin PDP Jam’iyyar DPP ta ci zabe a wannan karamar hukuma, amma suka ki rantsar da ’yan DPP masu wannan korafi idan ba su yi haka ba, za mu yi mamaki domin su ’yan adawa ne. Kuma a cikin mambobin kananan hukumomin da aka rantsar akwai ’yan PDP a ciki.

Wadanne nasarori kake ganin Gwamna Lalong ya samu, tun daga lokacin hawansa zuwa yanzu?

Babbar nasarar da Gwamna Lalong ya samu a Jihar Filato, ita ce zaman lafiya. Domin kowa ya san an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, a Jihar Filato. A da kafin zuwan Gwamna Lalong idan karfe 5 ta yamma ta yi, ba ka isa ka bar gidanka ba.

A yanzu za ka kai karfe 12 dare kana yawonka, babu abin da zai dame ka. A da zuwa gona ya gagari al’umma, amma yanzu kowa yana tafiya gona abinci ya bunkasa, a jihar nan. Idan ka dawo bangaren masana’antu ga su nan, an bude masana’antar taki, an bude masana’antar yin ruwan kwalba a Barikin Ladi da sauran abubuwan ci gaban jihar da dama.

Wane sako kake da shi ga al’ummar Jihar Filato?

Sakona ga al’ummar Filato shi ne mu hada kai, mu kaunaci junanmu, Kirista da Musulmi da wanda ba ya da addini, mu hada kai mu kaunaci junanmu don ci gabaanmu.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya