✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kuskure ne mace ta raina sana’a ko riba – Maryam Suleiman

A tattaunawa da Aminiya, Hajiya Maryam Suleiman mai masana’antar hada kek na Shuk Cakes da ke Kaduna, ta ce kuskure ne mace ta raina sana’a…

A tattaunawa da Aminiya, Hajiya Maryam Suleiman mai masana’antar hada kek na Shuk Cakes da ke Kaduna, ta ce kuskure ne mace ta raina sana’a ko riba. Kuma ta bayyana yadda mata za su iya hada neman ilimi da aure da yadda shafukan sada zumunta na zamani ke taka rawa a tallata hajoji da kuma fadi-tashinta a rayuwa:.

 

Tarihina

Sunana Maryam Suleiman, an haife ni a birnin Kano. Ni ce wacce ta kafa kuma Shugabar Kamfanin Shuks Cakes da ke garin Kaduna.

 

Ilimi

Na yi ilimin firamare har zuwa sakandare a birnin Kano. Daga bisani bayan na gama sakandare na yi aure na dawo Kaduna da zama, wanda a nan ne na ci gaba da karatu a Jami’ar Jihar Kaduna, inda na karanci ilimin tarihin kasa (Geography). Na yi hidimar kasa a Kaduna a shekarar 2015.

 

Burina ina karama

Burina ina karama bai wuce in ga na zama kamar mahaifiyata ba, wadda tana matukar son girke-girke da karance-karancen littattafai.

 

Abin da nake kewarsa

Ina kewar yadda rayuwa take a lokacin nan. Akwai kwanciyar hankali, akwai zumunci na tsakani da Allah da dai sauran abubuwa da suka yi wahala a yanzu.

 

Kalubalen rayuwa

Babban kalubalen da na fuskanta a rayuwata bai wuce rashin mahaifiyata da na yi ba a cikin kananun shekaru. A kowane lokaci ina matukar kewarta.

 

Nasarorina

Alhamdulillah Allah Shi ne Abin godiya a koyaushe. Na samu nasarori tunda har sana’ar nan za ta rufa min asiri, wani ma ya amfana da ita, to kuwa nasara ce babba a wurina. Misali a lokacin da na fara sana’ar nan ina yin ta cikin gida a kicin dina; kuma duk yawancin abubuwan da nake amfani da su na amfanin gida ne. Wasu ayyuka sau tari sai dai in yi da hannu saboda ba ni da kayan aiki, amma yanzu alhamdulillah kusan in ce ina da duk wani muhimmin abu da ake bukata, na mallake shi, wanda kuwa babbar nasara ce.

 

Dalilina na shiga sana’ar girke-girke ko hada kek

Sha’awa ce ta sa ni shiga fannin. Kuma na yarda cewa duk abin da za ka yi shi don kana sonsa kana sha’awar shi to tabbas za ka jure duk wani kalubale da za ka fuskanta ta dalilinsa. A koyaushe na samu odar kek nakan kasance cikin farin ciki domin ina son in yi in ga kuma yadda abokin ciniki zai ji dadi.

 

Abin da ya fi faranta min rai a sana’ar da nake yi

Manyan abubuwan da suke faranta min rai a sana’ar kek suna da yawa. Sana’ar tana sa min nishadi a koyaushe, ta samar mini da aikin dogaro da kai ba tare da jiran gwamnati ba, babban abin da yake kara burge ni da sana’ar shi ne yadda za ka ga mutane suna sha’awarka, suna karfafa maka gwiwa a kan ka kara rike sana’ar domin sana’ar hannu ita ce tabbas.

Abin da nake son a tuna ni da shi

Ina so a tuna ni da wata baiwar Allah wadda ta inganta rayukan mutane da dama a fannoni daban-daban. Zan so nan gaba a ce ina da wata ’yar kungiya ta koya wa matasa irin wannan sana’a ta yadda za su dogara da kansu ko da kuwa ba su samu ilimi mai zurfi ba.

 

Shawarar mahaifiyata da ba zan manta da ita ba

Na rasa mahaifiyata ina karama, lokacin da take raye nasiharta ba ta wuce ki yi abota da mutanen kirki, kuma ki yi gaskiya a duk halin da kika tsinci kanki ba.

 

Tufafi, turare, jaka da takalmin da na fi so

Ta fannin tufafi ina son atamfa da leshi. Turare kuma duk wanda ya yi mini dadin kanshi, haka jaka da takalmi duk wanda ya yi mini kyau zan saka.

 

Yadda nake hutu

Ina zama tare da iyalina; mu yi wasa da dariya.

 

Yadda na hadu da mijina

Na hadu da mijina ina aji biyar a sakandare, duk da dama muna da alaka ta ’yan uwantaka da shi. Hakan ne ya sa ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba manya suka shiga maganar. Bayan na gama makaranta da ’yan watanni aka daura mana aure.

 

Abin da na fi so daga mijina

Ina son komai daga mijina, saboda shi ne babban abokina. Ina son yadda yake ba ni kwarin gwiwa a kan duk abin da na sa a gaba, kasancewata tare da shi na daya daga cikin abin da yake faranta mini rai a koyaushe.

 

Iyalina

Ina da ’ya’ya uku – maza biyu mace daya.

 

Mawakan da na fi so:

Mawakanmu na Hausa, musamman wakokin Umar M. Sheriff.

 

Abincin da na fi so

Shinkafa, ba na iya kwana biyu ban ci ba.

 

Kungiyoyin da nake ciki

A yanzu ba na cikin wata kungiya, amma nan gaba ina burin kafa kungiya ta kaina.

 

Gudunmawar da nake bayarwa

Ina bayar da gudunmawa sosai ga yara matasa, domin lokuta da dama mutane za su kalle ni su ce burinsu su zama kamar ni. Yadda nake gudanar da sana’ata, ina koyar da mutane sana’ar kek, ina kuma daukar masu taya ni ayyuka kan sana’ar wadannda wadansu ta haka suke rufa wa kansu asiri, alhamdulillahi.

 

 Shawarata ga mata

Babbar shawarata ga mata ita ce a dage a yi ilimi a kuma ko yi sana’a, abin da ya sa na ce ilimi a farko, shi ne sana’o’i yanzu suna tafiya tare da ilimi ne, zamani ya canja sosai, tallata sana’a ta ta’allaka ce yanzu ta kafafen sada zumunta na Intanet, amma duk da haka koda a ce ilimi mai zurfin bai samu ba, ba zai hana mutum dogaro da kansa ba.

Babban abin da ake bukata kuma shi ne jajircewa da hakuri, sannan ka mika lamuranka ga Allah ta jijircewa da addu’ar neman albarka a koyaushe. Babban kuskure ne mutum ya raina sana’a ko kuma ribarta da sannu-sannu komai yake farawa.

 

Hada karatu da aure

Kwarai mata na iya hada karatu da aure, domin ni ma haka na yi karatu da aure. Bayan aurena da mako uku na fara zuwa makaranta, akwai wahala kam, domin abubuwa za su rika yawa, ga goyon ciki ga raino ga makaranta duk a lokaci daya. Amma babban abin da a kullum za ka kudurce a ranka shi ne wata rana zai zama labari kuma bayan duk wata wuya akwai dadi insha Allah.