Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kuskuren da ake yi game da sakin aure (3)

Assalamu Alaikum ‘yan uwa masu albarka masu bibiya ta a cikin wannan fili na iyayen giji da fatan Allah Ya kara mana juriya da hakuri sannan Ya amfanar da mu  baki daya.

 

ADVERTISEMENT

Shin ya halarta iyaye su sakarwa dansu mata?

A ‘yan kwanakin nan an samu tirka-tirka a wasu garuruwa kamar yadda na ji wani ya yi kira kai tsaye a cikin wani shiri a wata kafar yada labarai da kuma wasu bayin Allah da suka kira ni a mabambanta garuruwa cewar “mahaifan su sun saki matar ‘ya’yan su ba tare da amincewar su ba kuma har sun gama idda sun auri wasu a matsayin mazaje, shin ko wannan aure na baya ya inganta?

ADVERTISEMENT

Ko shakka babu hakkin iyaye na daya daga cikin manyan hakkoki da Allah Ya yi magana, haka aure na daga cikin sunnar kowane Annabi da Allah Ya aiko bisa doron kasa, har Annabi SAW yake cewa “ Aure sunnah ta ne kuma duk wanda ya kyamace ta ba ya tare da ni”.

Amma duk da girman wannan hakki na iyaye Allah Bai rataya saki a hannun su ba.

MUTANEN DA SHARUDDAN SAKI BA SU RATAYA A WUYAN SUBA:

Bari mu ji wasu halaye biyar da shari’a ta ce in mutum ya saki matar sa a wadannan halaye ba ta saku ba.

1- Sakin mutumin da aka tilasta; dole ne miji ya kasance mai ra’ayin kansa, idan kuma har wasu za su yi amfani da matsayi na jini ko kusanci ko kuma karfi na mulki a bisa tilasci a sakar wa mutum mace to ba ta saku ba,ciki har da iyaye.

Sai dai mafi kyawu a duk lokacin da mahaifan mutum suka nuna masa ba su son wani abu, sai ya bi hanyar da ta dace don fahimtar da su ta yadda za su amince da abin in kuma har suka cije a kan sai ya yi abin sai ya dubi girman darajar su da suka yi silar samar da shi a bisa doron kasa ya yi masu biyayya don neman yardar Allah.

2- Sakin mahaukaci; wannan ma wani abu ne sananne a shari’a cewar hankali na daga cikin sharuddan karbar ko wane irin aiki na ibada.

3- Sakin mutumin da ke cikin maye; wasu malaman na ganin ta saku saboda shi ya sanya kansa a halin mayen, amman wasu malaman na ganin matar ba ta saku ba saboda akwai hukuncin da Allah Zai yi masa a kan shan kayan mayen da ya yi. Allah Ne mafi sani.

4- Sakin marar lafiya wanda ya kai gargara; malamai sun yi magana cewar “idan har ya saketa ne da gangan don ya hana ta cin gado to ba ta saku ba in kuma ita da kanta ta nema ko kuma ta yi laifin da yana iya kai wa ga saki shi ma wasu malaman na ganin ta saku.

5- Sakin da aka yi cikin zuciya ba tare da furuci ba. Mafiya rinjayen malamai sun tafi a kan wannan saki bai inganta ba saboda fadar Annabi SAW da ya ce “lallai Allah Ya yafe wa al’ummata abin da zukatansu suka ambata muddin ba su furta ko suka yi aiki da shi ba.”

Don haka ina kira ga iyayen da suka aukar da irin wannan saki da mazajen da aka sakar wa matan da ma wadanda suka aura da dukkanin al’ummar musulmi da mu ji tsoron Allah sannan mu tuntubi malamai, don gaskiya akwai ganganci kuma za a rika afkawa cikin zina da gangan.

Da fatan Allah Ya shiryar da mu bisa tafarki na kwarai. Sai mun sake haduwa a wani darasin in Allah Ya yarda.

Sanusi Hashim Abban Sultana daga Jihar katsina. sanusihashim3@gmail.com, 08065507271