✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kusukure ne a ce kada Jonathan ya fito takara – Maikudi Tela

Shugaban Yakin Neman Zaben Shugaba Jonathan da Namadi Sambo a Jihar Kaduna, Alhaji Maikudi Tela ya ce kuskure ne wasu ’yan siyasa ke yi da…

Shugaban Yakin Neman Zaben Shugaba Jonathan da Namadi Sambo a Jihar Kaduna, Alhaji Maikudi Tela ya ce kuskure ne wasu ’yan siyasa ke yi da suke cewa kada Shugaba Jonathan cewa kada ya fito takarar kujerarsa a zaben 2015.
A cewarsa, tunda har dokar kasa ba ta hana Shugaba Jonathan tsayawa takara ba, bai ga dalilin da wani zai nemi hana shi takara ba.
Alhaji Maikudi Tela ya bayyana hakan ne a zantawarsa da Aminiya a Kaduna, inda ya ce ce fitowa takarar Shugaba Jonathan da Mataimakinsa Namadi Sambo zai ba su damar kammala ayyukan alheri da gwamnatinsu ta fara.
“kungiyarmu ta gamsu da irin ci gaban da kasar nan ta samu a lokacin mulkin Jonathan da Namadi saboda haka muna nanata goyon baya gwamnatinsu ta ci gaba don kammala ayyukan raya kasa da tabbatar da zaman lafiya da suka sa a gaba. Wannan ne ya sa muke ganin kuskure ne masu nuna adawar gwamnatin ta ci gaba, saboda tsarin mulki bai hana Shugaba Jonathan sake tsayawa a zabe ba.  Tunda wannan gwamnati ta hau mulki ake samu cigaba a fannoni da dama tare da kokarin ganin an warware matsalolin da ke addabar kasa, musamman a tattalin arziki da tsaro,” inji shi.
Shugaban ya ce kamata ya yi a karkafa wa wannan gwamnati gwiwa ta yadda za a samar da ci gaban da ya kamata. Kuma ya yi gargadin cewa idan ba a yi hattara ba rashin tsaron da Arewacin kasar nan ke fama da shi na iya janyo karancin abinci a bana domin manoma na tsoron zuwa gonakinsu bisa la’akari da rashin zaman lafiya.
Ya ce babu wani ci gaba da kasa za ta samu a yanayi na rashin tsaro da kwanciyar hankali don haka yake rokon yan bindiga da su ajiye makamansu domin rungumar hanyar sulhu.
Ya bukaci jama’a su ba gwamnatin Jihar Kaduna goyon baya saboda ayyukan ci gaban kasa da take aiwatarwa a sassan jihar.