✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwadagon kwafar kadagon koto

Kokon kwafar koto Kulafacin karin kunto Kwakwar karajin kato Kulle-kullen kwarmato Kwadagon tereren toto   Mutane masu himma Na neman karin kima Turka-turka ta jima…

Kokon kwafar koto

Kulafacin karin kunto

Kwakwar karajin kato

Kulle-kullen kwarmato

Kwadagon tereren toto

 

Mutane masu himma

Na neman karin kima

Turka-turka ta jima

Ana ta fama

Wasu na ta fankama

 

A daukacin al’umma

’Yan tsiraru ke shan zuma

Gama-gari ga gumama

Ana ta hauma-hauma

Jikon jikaken tsumma

 

Kimar kudi

Ta haifar da radadi

Masana tattali ai budi

Malumma ai ta gargadi

Taska na da mabudi

 

A cikin lalama

Ake taho mu gama

’Yan kwadago ina makama

Yaji-gautan gardama

Mahukunta na ta lalama

 

Ijarar aiki ake takamma

Tsadar kaya ba alama

Gwamnati ai himma

Talakawa na hamma

A tsahirta da zalama

 

Masu gyara ai azama

Jami’an hukuma

Ga aiki a bazama

Masalaha babu tantama

A taho masana malumma

 

Na fasko wannan rigima

Mui azama

Kar ajima

Ana ta tuhuma

Manufa dai fita daga duma

 

Kurkura karmar kumbula

Kundunbalar kwalamar kwandala

Karajin karin kila-wa-kala

Kulunboton kwalla

Koton kakalen kwaila

 

Sandar samfewa da sulalla

Surkullen shakar kwala

Sukuwar aura da mangala

Sukur-sukur din talge na sulala

Sare-sarin shagalin shagalla

 

Gantalin gaula

Gararambar gafala

Gagarumar gudumar gula

Ganin galala

Gwangwaje galleliyar galila

 

Kwadon mandako

Gararamba da dan koko

Kwaki da karago aka jinko

Ja-in-jar sunkurun sako

Tariyar baya a fako

 

Magagin mai makoko

Rakin rarrashin roko

Mummunar  fahimta da riko

Mirgina-mirginar lasar maiko

Jaga-jagar jinkar jiko

 

Dubun nunin saman babban lauje

Dumbujen kauje

Dungun dauje

Dundumin  jaje

Dagar da’irar saje

 

Ladar kwadago

La’adar kadago

Laulawar  hannun agogo

Lallami mai kwanan shago

Lallashi amarya da ango

 

Haurobiyawa ai awo

Juye-juyen kai-kawo

Kandamar damun dawo

Don jin dadin yawo

A samu miyar cin tuwo

 

Magabtanmu

Makiyan magabatanmu

Su ke tauye mu

Sun hana  neman nakanmu

Har a rasa hatsin tumu

 

Baba a ba da hatsi

Kowa ya daina tsi-tsi

An tauna gurin guntsi

Kashi na da gautsi

Ko na kaza mai fatsi-fatsi

 

Kar a karke da yamutsi

Akwai tsokana da latsi

Ruwan rijiya na da zartsi

Hargowar haifar da hargitsi

Ai kokarin fita daga matsi

 

Sai a tallafi rayuwa

Mafi yawan talakawa

An bar su suna kwaruwa

Al’amura su zam gyaruwa

Ko a daina cutuwa

 

Masu mulki

Ai aikin kirki

Miyagu a taka musu burki

Mabukata a ba su a masaki

Ka da kowa yai raki

 

A biya Bokan Turai

Don ceton rai

Masu jinya ko jira-jirai

Uwar jiki tai kyau sarai

Wannan shi ne aikin kwarai

 

Ina Direban alli

Koyar da mu dabarar asali

Juhala a yanketa da kansakali

Darussa ai musu jaddawali

Koyi ka koyar a kowane hali

 

Lallai ai masalaha

Rayuwa ta dan yi arha

Da jin dadin shan gahawa

Babu bare balle bawa

Kowa-da-kowa ai ta raha

 

A daidai lokacin da zabi-sonka na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa ke karatowa, ana ta ZAKWADIN ZUMUDIN ZUNGURO ZUNGURUN ZAZZAGA DA ZUGA-ZUGIN ZUGAR ZAGAYE-ZAGAYE, inda ake ta faman tufka da warwara a kasar nan, musamman in an yi la’akari da turka-turkar takaddamar karin lada da la’adar kadagon kwadago da aka yi fama da ita cikin makonin da suka rare a guje. Kodayake kare-karen tsare-tsaren inganta rayuwar al’umma na da dadi, amma karin kudi na iya haifar da rudanin radadi, musamman idan darajar kudi ta fadi.

Haurobiyawa, sanin kowa ne a kasar nan tsallen badaken ’yan kwadago ba sabon al’amari ba ne. Don haka nake ganin lokaci ya yi da za a yi wa tufkar hanci, ko masu fafutikar laluben na-koko a ma’akatun gwamnati da kamfanonin kamfatar dukiya masu zaman kansu sa fice daga kunci.

Wajibi ne a kan kungiyoyin kwadago su san hakikanin abin da suke neman tabbatarsa, matukar dai ba rashin tabbas suke fafutika a kai, wadda ka iya haifar da: Gantalin gaula Gararambar gafala da Gagarumar gudumar gula da Ganin galala don Gwangwaje galleliyar galila.

’Yan makaranta masu koyon watsatsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, mu yi wa kawunanmu masalaha, ta yadda tallafin tallafar harkokin rayuwa zai inganta walwala, ya kange mu daga wala-wala, don ta haka ne kawai hada-hadar harkoki za su yi arha, kowa-da-kowa ai ta raha.

Lallai a daina duk wani kulafucin kulle-kullen munafunci, domin su ke kara ingiza a’umma su afka cikin kunci.

Batu na ingarman karfen karafan titin tarragon layin dogo, ba tare da bata lokacin wulwulawar agogo ba, ’yan kwadago a himatu ka’in da na’in wajen ganin an inganta FARFAJIYAR KOYON WATSATTSAKE DA BUDA WAGAGEN LITTATTAFAI ta ’yan dugwi-dugwi, kuma a yi namijin kokarin kyautata farfajiyar Bokan Turai, don tarairaya da ceton rai; jami’an tsaro a tura su kwararo-kwararo, don shawo kan yanayin kasa na BA TSARO SAI TSORO, lallai a kara musu horo.

Tabbas aiwatar da managartan tsare-tsaren da na ambata a darasin makaranta, da ma wadanda ban ambata ba, za su yi matukar taimakawa wajen warware turka-turkar takaddamar turnukun tarnakin takun Kwadagon kwafar kadagon koto!