✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwaikwayon al’adun Turawa na gurbata namu – Victoria Mamuda

Darakta a Ma’aikatar Al’adu ta Jihar Gombe Misis Bictoria Usman Mamuda ta ce kwaikwayon al’adun  Turawa da wadansu mutane da kalle-kallen wayoyi ya sa yaran…

Darakta a Ma’aikatar Al’adu ta Jihar Gombe Misis Bictoria Usman Mamuda ta ce kwaikwayon al’adun  Turawa da wadansu mutane da kalle-kallen wayoyi ya sa yaran yanzu suke tashi ba su da al’ada tare da mantawa da al’adunsu na gargajiya.

Bictoria Mamuda, ta bayyana haka ne a wajen bikin Al’adun Gargajiya na Kabilar Pero a Karamar Hukumar Shongom a Jihar Gombe karo na 4 da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata a Kurmin Yafuro a garin Gwandum wanda aka yi wa take NAKKA.

Daraktar ta yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabanin al’umma su rika tsawatar wa mabiyansu suna tsayawa wajen koya wa ’ya’yansu al’adunsu na gargajiya don kauce wa tashi cikin rashin sanin al’adunsu.

Ta kuma ce kamar yadda ’yan kabilar ta Pero suka nemi a ba su wani lokaci a gidan rediyon Jihar Gombe don gudanar da shirye-shirye da harshensu na Pero ta ce za ta yi magana da Kwamishinan Watsa Labarai kuma tana tabbatar musu insha Allah hakan ba zai zama da matsala ba.

Da yake jawabi a wajen bikin, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na Jihar Injiniya Abubakar Bappah ya ce wannan karon taron ya kayatar domin ba kamar wanda aka yi a baya ba.

Injiniya Bappah ya ce a lokacin bikin suna nuna kayayyakin al’ada da raye-rayen gargajiyarsu na al’ummar Gwandum, wanda hakan yakan sa yara da suke tasowa suna sha’awar al’adunsu domin kada sai sun girma su rasa al’ada su su rika kame-kamen al’adun mutanen ketare wanda ba zai taimake su ba a rayuwa.

Dagacin Gwandum Malam Yahaya Haruna JP, cewa ya yi makasudin gudanar da wannan biki na al’ada shi ne don ’ya’yansu da jikoki su tashi da son al’adunsu na gargajiya.

Ya roki Gwamnatin Jihar Gombe ta samar musu da hanya domin garin Gwandum yana iyaka da garin Gobirawa a Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi don saukake wa mutanensu zirga-zirga.

Bako na musamman a wajen Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe Alhaji Sadik Ibrahim Kurba, jinjina wa al’ummar Gwandum ya yi kan yadda suka rungumi al’adunsu na gargajiya.

Alhaji Sadik Kurba, ya ce ko a majalisa, dan majalisarsu Samuel Markus a kullum idan ya tashi damuwarsa ita ce yaya za a yi a taimaki al’ummarsa a ciyar da yankinsa gaba.

Mataimakin Gwamnan Jihar Mista Manasseh Daniel Jatau, cewa ya yi al’ummar Gwandum sun burge shi domin sun rungumi al’ada don duk wanda bai da al’ada ba ya da asali.

A loakcin bikin yara ’yan firamare sun gabatar da taken Najeriya da yaren Pero sannan an gudanar da wasannin gargajiya daban-daban da raye-raye da kade-kade.