Da Dumi Dumi

Kwaikwayon fim kin zanen takala ya sa yaro ya diro daga bene hawa 10

Wani yaro kan shekara 10 ya diro daga bene mai hawa 10, ta hanyar amfani da lema, kamar yadda kafafen yaka labaran kasar Sin suka ruwaito. Yaron kan shekara bakwai ya yi tsallen ne bayan da ya ga wani fim kin zanen takala da ya nuna wani ya diro daga sama ta taga, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar South China Morning Post ta ruwaito cewa iyayen yaron suna zaune ne a hawa na biyar a gidansu da ke Suzhou a gundumar  Jiangsu, wanda aka kimanta tsawonsa da hawa 10 na jerin gidajen da ke kasa.

Wani abin mamakin ba lemar ba ce ta cece shi, illa dai kawai wata wayar lantarki da ya fako kanta, wadda ta kange shi daga tuntsurowa, kamar yadda wanda lamarin ya auku a gabansa ya bayyana. Mahaifiyar yaron da ta ga kanta a cukwikuye a kasa, sai ta zube a kasa. Yaron dai wanda ba a ambaci sunansa ba, ya samu raunuka, kamar yadda likitoci suka bayyana.

ADVERTISEMENT

Kafar yaka labarai da ke kan shafin intanet  na Sohu.com ta ruwaito yadda kananan yara ke ji wa kansu raunuka ta hanayar kwaikwayo harigidon fina-finan zanen takala na ‘Cartoon.” Yaran  da ke kwaikwayon ganganci na hakurra daga fina-finan talabijin sun haifar musu da munanan raunuka kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A Maris kin da ya gabata, wata yarinya ’yar shekara biyar an yi saurin kai ta wajen kula da lafiya na gaggawa bayan ta yi amfani da lema ta dirko daga hawan bene na 11 a wsani ginin Urumki da ke Kianjiang, inda fako a kan hawa na huku. Haka cikin Disambar bara, wata yarinyar ta hau kan bututun ruwa da ke wajen gidansu a hawa na biyar, inda ta fako t aji munanan raunuka.

Wakannan al’amura da ke ta faruwa sun sanya ana ta tafka mahawara kan ko gwamnati ta kakaba doka kan fina-finan da suka dace yara su rika kallo gwargwadon kimar shekarunsu, kamar yadda ake da irin wakannan dokoki a kasashen Yammacin Turai.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya