Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Kwakwar karin kadagon kwadago

Kwakwar karin kadagon kwadago

’Yan kwadago

Suka kai bango

Tsallen gajere da dogo

Karin ya zamo lullubin bargo

Mahankalta sun hango

 

Dubu kofar hancin zagayen zango

Ana ta duban agogo

Wasu har sun waigo

Ba gara bin zago

Da wace siga aka shigo

 

La’akarin farashin tunkuza

Yai ta gurza

Ana tataburza

Turka-turka ta turza

Carin carar zakara da kyarkyarar kaza

 

Ana ta kasafin kudi

Wasu sun samu budi

Yawan matsabbai mai rudi

Shudi-shudi da rodi-rodi

Watangaririyar juyin rawar kodi

 

Tsandarewar tsawalar tsada

Tsamin tsotsar tsada

Gada-gadar gudun gada

Garambar gargada

Tungar taga-taga  ta tada

 

Sha’awar shunin shadda

Sanya suturu masu tsada

Faden fatar kada

A ci a sha ai hani’an

Hidindimu ka’in da na’in

Kauce-kaucen wahalar borin na-kada

 

Wasu na wadaka

Wasu na ta kaka-kaka

Wahalhalu fara da baka

Hatsi na bukatar nika

Markaden miya sai an jika

 

Baban-burin-huriyya

Kari ai tariya

Ai tarairaya

A kyautata aikin neman na miya

A kiyayi zamiya

 

Malam Na-Agege

Kai dagar doge dudduge

Wasu na ganin ka burge

Na ga wasan bera da mage

Kar dai kare-kare su sage

 

Lalurar dan tsito mai cizo

Tana haifar da kwakwazo

Cuta mai gizo

Da ke hana dandanar kanzo

Da zarar zoginta ya furzo

 

Ana ta bikin ranar kwadago

Masu murna sun tattago

Zuga-zugi sun zazzago

Cisge sasari tuni an cisgo

Burgar buge-buge ta bubugo

 

Hakkoki sai an kwato

Dokoki a karanto

Aiki da hankali a halarto

Komai daki-daki loto-loto

Kyautayi a kyautato

 

Masu bin kadin lamuran da ke wakana a fadin Haurobiya sun dade suna tsokacin tsokale-tsolen TSANDAREWAR TSUGUDIDIN TSAWWALAR TSADA TSAGWAGWA, daidai lokacin da ake ta fafatawar fafutikar KUGIN KARIN KADAGON  KWADAGO, inda kungiyoyin kwadago suka yi ta turka-turkar tarairayar tarin tumun tumar tumurmutsa matsabbai. Babban dai abin gudu, ko ma abin ki  shi ne ka da a nunke ’yan kwadago a baibai har su farga su fara DAWUWURURIN DAMBARWAR DULMIYEWAR DUBE-DUBEN DUBBBAN DIRHAMOMIN DALOLIN DUBAI DAGA DABAI.

Ko ma dai mai hukumomi suka tsuwurwurta a irin yarjejeniyar da suka kulla da kungiyoyin kwadago kan karin kadago, wajibi ne a yi la’akari da al’amuran da ka iya yunkurowa su bijiro a tsakankanin masu hada-hadar safarar sarrafa dukiya a kasuwannin kasar nan. Kuma su ma masu laluben kadago a wajen kwadago akwai bukatar su iya tsara tsarin rayuwarsu ta yau da kullum ‘daidai ruwa, daidai tsaki.’ Ka da kurum daga ganin an dumbuzo wa mutum damin matsabbai, sai kawai ya nunke kansa a baibai, wai yana Sha’awar shunin shadda da sanya suturu masu tsada, tare da kakaba faden fatar kada; sai a ci, a sha ai hani’an da hidindimu ka’in da na’in ba tare da dabarbarun  kauce-kaucen wahalar borin na-kada ba.

Wannan makaranta ta Dodorido da ke cikin Amintaciyar jaridar kasar Haurobiya ta bijiro wa masu koyi-ka-koyar a fannonin watsattsake da falle shafukan mujallu da makalu da jaridu da wagagen littattafai wannan turka-turka ta KUNDUNBALAR KUGIN KARIN KADAGON  KWADAGO, ganin an yi bikin murnar zagayowar ranar ’yan kwadago ta duniya a kasar Haurobiya. Sannan a ankarar da hukumomi da jami’an Gwamnatin Baban-burin-huriyya, musamman Malam Na-Agege cewa akwai sauran rina a kaba; don haka sai a yi mai yiwuwa don ka da bar baya da kura.

Batu na ingarman karafuna titin kwangiri layin dogo, akwai bukatar karin tallafin tarairayar harkokin rayuwa fiye da karin kadagon kwadago. Domin ta haka ne kawai karin kadago zai yi tasiri tasirifin juyi mai alfanu, dibge da dimbin fa’idojin inganta rayuwar al’umma a fadin kasar nan. Duk wata dabarar da ya kamata a yi wajen ganin ba a koma turakar jiya ba, wajibi ne a yi, kususan in an yi la’akari da cewa, ‘ lokacin da ma’aunin farashin man tunkuza yake kan Hauro madambaci da hauya, kimar adadin lita da ake iya saye daga lalitar da ke dibge da mafi karancin karin kadagon kwadago na sili da madamci duk bai wuce dari karamin lauje da hauya ba; sannan masu bin didigin al’amura, sun sake zuba alkaluman lissafin, inda suka fasko cewa daidai wannan lokaci da aka yi karin DUBUN KOFAR HANCI DA ZAGAYE, yayin da litar man tunkuza ke kan farashi dari sili da tsayuwa bisa kafa guda da babban lauje, ana nan a turka-turkar turakar jiya (i yau), wato dai LALITA da ke dibge da mafi karancin karin kadagon kwadago, za ta iya cefano LITA dari karamin lauje da hauya ne kacal.

Tuni dai an baza irin wadanan bayanai a shafin watso-zuffa, watakila ma wasu sun baza shi a shafukan FUSKANTAR-BOKOKO da TUKIN-TUWON-TITI da makamantansu. BOKAN-TURAI a tarairayi rai; Direban-alli a nusar da dalibai aiki da hankali, masu kasuwanci ban da kaso-kason wawanci ko cutar masu neman rahusar kayan masarufi don gudanar da harkokin yau da kullum.

Haurobiyawa da hukumomi da kungiyoyin kwadago sai a hada karfin karafun wajen shawo kan kowace irin tashintashina, don gudun ka da a karke da cewa an yi BAYA BA ZANE!