Search
Subscribe
Kwalekwale ya kife da ‘yan mata 6 a Kebbi

Kwalekwale ya kife da ‘yan mata 6 a Kebbi

Wani kwale-kwale ya kife da ‘yan mata shida a kauyen Tindifai da ke gundumar Dakingari a Karamar Hukuman Suru ta jihar Kebbi a jiya Talata.

Matan da kwale-kwalen ya kife da su sun hada da: Hadiza Garba mai shekara 15, Lauratu Muhammad, mai shekara 13, Adama Musa mai shekara 15, Firdausi Garba mai shekara 13, Maryam Abdullahi AbdulRahnan mai shekara 13 da Suwaiba Abdullahi AbdulRahama mai shekara 10.

Direban kwale-kwalen mai suna Umar Faruk dan shekara 13 ya ceto mutum uku daga cikin kwale-kwalen. Kwale-kwalen ya kife ne lokacin da suke hanyarsu ta zuwa gona don girbe shinkafa.

Sakatarenm watsa labarai na Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Mu’azu Dakingari, ya ce a yanzu haka an gano gawarwaki 5 na fasinjojin kwalekwalen, yayin da ake ci gaba da neman sauran ‘yan mata shida a cikin kogin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin