✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalliya da rigar sanyi

Rigar sanyi kamar yadda sunan ya nuna ana sanya ta ce don ta kare jikin mutum daga sanyi, sai dai ba lokacin sanyi kawai ake…

Rigar sanyi kamar yadda sunan ya nuna ana sanya ta ce don ta kare jikin mutum daga sanyi, sai dai ba lokacin sanyi kawai ake iya sanya ta ba. A duk lokacin da yanayin gari ya canja, ma’ana aka samu kadawar iska, don haka ana iya sanya ta a lokacin damina.

Baya ga irin taimakon da rigunan sanyi ke yi wa mutum ta hanyar dumama masa jiki da kuma kare shi daga sanyi, sanya rigar sanyin kan zama wani abin kwalliya ga mutum. Domin akwai wadansu da ake iya sanyawa a lokutan shakatawa, musamman da daddare.

Ana iya samun irin wadannan rigunan sanyi cikin yanayi da launi daban-daban, wanda idan har kina bukata za ki iya zabar launin da zai dace da irin kayan da kike sanye da su. Irin wadannan rigunan sanyi akwai wadanda ake saka su da hannu akwai kuma na inji.

Ana kuma samun rigunan sanyin a rufe gaba daya, wasu kuma suna zuwa da maballai a gabansu, ta yadda mutum zai iya bude su ko kuma ya rufe su idan yana bukata.

Tsarin yanayin wuyan rigunan ma iri-iri ne, yayin da wasu sukan zo da tsarin wuya a kewaye, wasu kuma sukan zo da alamar gwafa. Haka kuma tsarin hannun rigar shi ma yakan bambanta, akwai mai dogon hannu da kuma mai gajere.