Da Dumi Dumi

Kwalliya lokacin damina

Mata da dama ba su cika son yin kwalliya a lokacin damina ba. Domin suna tsoro kada a fara ruwan sama ya wanke musu kwalliyar ko kuma ya cabe musu fuska. Sau da yawa ana tambaya shin wace kwalliya ce ta dace a yi a lokacin damina? Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a magance wadannan matsalolin cikin sauki.

• Akwai wasu irin hodar fandesho masu santsi kamar mai. Irin su ne ya kamata a yi amfani da su lokacin damina, domin ko da ruwan ya taba fuskar, ba zai wanke fuskar ba. A nemi irin wannan hodar fandesho domin samun sauki ga lamarin

• Akwai waterproof mascara abin nufi a nan shi ne ruwa ba ya ratsa cikinsa. Irinsa ne ya kamata ’yan mata da manyan mata su rika amfani da su a wannan lokaci. Idan ba a samu irin wannan mascara ba to a sani cewa kwalliyar za ta cabe sosai.

• Kada a manta da lema a duk lokacin da za a fita domin ba za a san lokacin da ruwa zai sauko ba.

• A kasance akwai abin rufe kai. Domin yawan sanya ruwa a gashi ba karamar karya gashin yake ba, don haka sai a samo wani abu da zai rufe kan yadda ruwan ba zai ratsa shi ba.

ADVERTISEMENT

• Yana da kyau kuma a san irin takalmin da za a sa saboda jikewa daga ruwan sama. Ana son amfani da takalmin roba wanda ba zai sa a fadi ba saboda santsin wuri sakamakon ruwan sama.

• A samu tufafi mai mutunci da za a sa a wannan lokaci saboda wani lokaci idan aka jike kuma in har tufafin ba na kirki ba ne sai a ga surar mutum ta bayyana a fili. Yana da kyau mace ta san yadda za ta kula da kanta.

Share