✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kwallon kafa na samun cigaba a Najeriya, amma…… Koci Salisu Yusuf

Shahararren mai horar da wasan kwallon kafa, Salisu Yusuf ya bayyana cewa harkar kwallon kafa tana samun ci gaba a Najeriya a halin yanzu. Sai…

Koci Salisu YusufShahararren mai horar da wasan kwallon kafa, Salisu Yusuf ya bayyana cewa harkar kwallon kafa tana samun ci gaba a Najeriya a halin yanzu. Sai dai kuma ya ce rashin tsari nagari na neman hana harkar kwallo cigaban da ya dace a kasar nan. 

Koci Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da wakilin Aminiya a Kano. Ya ce “a zahirin gaskiya kwallon kafa na samun ci gaba a Najeriya sannan kuma da akwai kyakkyawan fata ga kananan kungiyoyin kwallon kafa masu tasowa a fadin kasar nan musamman idan aka yi lala’akari da yadda a halin yanzu Najeriya ce kan gaba a fagen kwallo a Nahiyar Afirka. Akwai alamar Najeriya za ta samu hayewa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa sannan ga shi kungiyar kwallon kafa ta matasa ta ’yan kasa da shekaru 17 ta sake lashe kofin duniya na matasa a karo na hudu.”
Ya ce a halin yanzu an fara samun cigaba a harkar yin alkalanci a gasar rukunin Premier na kasa, yin haka kuma ba karamar cigaba aka samu a harkar kwallo ba. Ya ce a shekarun baya, abin ba haka yake ba don kulob da dama kan yi amfani da alkalan wasa wajen yin coge ne.