✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamandan Boko Haram ya mika wuya ga sojoji

Kwamandan Boko Haram Adamu Yahaya wanda aka fi sani da Sa’ad Kami ya mika kansa ga sojojin Najeriya. Sa’ad Karami shi ne Kwamandan Boko Haram…

Kwamandan Boko Haram Adamu Yahaya wanda aka fi sani da Sa’ad Kami ya mika kansa ga sojojin Najeriya.

Sa’ad Karami shi ne Kwamandan Boko Haram da ya jagoranci harin karshen da kungiyar ta kai wa sojoji a garin Bagan jihar Borno.

Yana cikin mayakan kuniygar da suka kai hare-hare a garuruwan Metele, Mairari, Bindiram, Kangarwa and Shetimari (Jamhuriyar Nijar).

Kwamandan yada labarai na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar John Enenche ya ye Adamu Yahaya ya mika kansa ga sojojin bataliya ta 242 ne sakamakon luguden bama-baman da suka tsananta kan mayakan kungiyar.

Sa’ad Karami ya mika kansa ne a ranar 24 ga watan Mayu kamar yadda sanarwar da Enenche ya fitar ta bayyana.

Sojoji sun ceto mutum 241 daga ‘yan Boko Haram

Manjo Janar Enenche ya kara da cewa sojoji su hallaka mayakan Boko Haram 12 sannan suka kubutar da mutum 241 da kungiyar ke tsare da su.

Mutanen da sojojin suka kubutar sun kunshi mata 105 da kananan yara 136 da a halin yanzu ake duba lafiyarsu.

Karin barnar da sojoji suka yi wa Boko Haram

Sanarwar ta ci gaba da cewa dakarun bataliya ta 151 sun kashe karin ‘yan Boko Haram masu yawa bayan wadanda suka tsere da raunin harbin bindiga.

Sojojin, inji shi sun murkushe lambon da mayakan kungiyar suka kai musu, suka kuma kwace motoci da manyan bindigogin kungiyar.

Sauran kayan da sojojin suka kwace sun hada da bindigogi samfurin AK-47 da FN Riffle da tarin harsasai.