Search
Subscribe
Kwamandan Makarantar Yaran Sojoji ya kaddamar da rijiyar burtsatse

Kwamandan Makarantar Yaran Sojoji ya kaddamar da rijiyar burtsatse

Kwamandan Makarantar Yaran Sojoji (NMS) da ke Zariya, ya kaddamar da rijiyar burtsatse mai injin bada wuta ga burtsatsen ga al’ummar  Unguwar Malam Sule da ke Gundumar Jushi Waje a Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.

Kwamandan Makarantar NMS, Manjo Janar Muktar Muhammad Bunza ya ce sun gina wa al’ummar da suke makwabtaka da makarantar rijiyar ce bisa bin umurnin da Babban Hafsan Sojojin Kasa,  Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayar na  a kyautata alaka tsakaninsu da fararen hula da suke makwabtaka da su. Ya ce wannan ba shi ne na farko ba domin a tsawon shekaru uku da ya yi a wannan makarantar ya samar wa mutanan kauyen Karau-Karau wajen da suke kai yaransu kwanan daji irin wannan rijiya.

Dagacin Jushin Waje Alhaji Abdullahi Tanko Sule, ya nuna jin dadinsa kan irin kyautatuwar  alakar da ke tsakanin al’ummar masarautarsa da makarantar yaran sojojin.

Dagacin ya yi alkawarin kula da rijiyar burtsatsen da aka yi musu don saukaka musu wahalar ruwa da suke fama da shi, tare da daukar nauyin kula da famfon.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin