✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin sulhunta Gabon da Amal ya fara aiki

Kwamitin mutum takwas a karkashin jagorancin Malam Khalid Musa da Mataimakinsa Sani Sule Katsina da aka dora wa alhakin sasanta jaruma Hadiza Gabon da Amina…

Kwamitin mutum takwas a karkashin jagorancin Malam Khalid Musa da Mataimakinsa Sani Sule Katsina da aka dora wa alhakin sasanta jaruma Hadiza Gabon da Amina Amal ya fara aiki gadan-gadan.

Daya daga cikin mambobin kwamitin, Malam Salisu Mohammed Ofisa ne ya bayyana wa Aminiya haka shekaranjiya Laraba, inda ya ce, kwamitin ya yi zama hudu da dukkan wadanda abin ya shafa, kuma ya fara zama na farko ne da lauyoyin Amal, sai na biyu da lauyoyin Gabon, na uku kuma da Gabon, sannan na hudu da Amina Amal.

Ya ce, a yanzu kwamitin wanda Kungiyoyin ’Yan fim ta Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) da ta Arewa Filmmakers Association of Nigeria (AFMAN) suka kafa zai yi zaman bai-daya da dukkan bangarorin da abin ya shafa. Ya ce, za a yi zaman ne don a sasanta ba tare da an danne wa kowa hakkinsa ba.

Idan ba a manta ba  a kwanakin nan masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood ta shiga rudani dalilin dora wani hoton tsiraici da jaruma Amina Muhammad wadda aka fi sani da Amina Amal ta yi a shafin sada zumunta na Instagram.

A hoton jarumar ta sanya matsattsun tufafin da suka fitar da surarta har da cibiyarta a waje, hakan ya sanya mutane suka yi Allah wadai da abin da ta yi, inda a ciki har da ’yan fim da suka hada da Hadiza Gabon da A’isha Aliyu Tsamiya da Hassan Giggs da Baballe Hayatu da sauransu.

A karkashin hoton da Amal ta sanya din ne Gabon ta rubuta ba da haka Amal za ta yi suna ba, inda A’isha Tsamiya ta ce abin da Amal ta yi ne yake sa a rika zagin Kannywood.

Sai dai bayan kwana daya sai Amina Amal ta sake sanya wani hoto a shafinta na Instagram mai dauke da wata hira, inda a karkashin hoton ta rubuta sai dai a kira ta karuwa saboda shigarta, amma ita ba ta madigo.

Wannan al’amari ne ya sanya aka fara zargin a masana’antar, inda aka wayi gari wani bidiyo mai tsawon minti 1 da rabi  yana yawo a kafar sada zumunta.

A bidiyon wanda aka dauka a juye an ga jaruma Amal zaune a kan katifa, inda wata murya da ake zargin ta Hadiza Gabon ce take umartar Amal ta karanta sakonnin da suka tura wa juna ta Instagram, inda hakan ya kai har da mari da duka.

Sai dai a bidiyon wani da aka kira Ustaz ya kira jaruma Gabon da Ustaziya, inda ya bukaci ta daina dukan Amal. A bidiyon Gabon ta yi addu’ar idan har ta cuci Amal to Allah Ya hana ta abin da take so duniya da Lahira.

Bayan haka ne wani bidiyo mai tsawon minti 1 da rabi  ya sake fita, a bidiyon an nuna Amal a wani shago, sannan jaruma Gabon tana yi mata tambayoyi. Gabon ta tambayi Amal ko ta taba nemanta da iskanci ko ta taba cutar da ita, inda Amal ta amsa da a’a.

Amal ta ce sharrin Shaidan da shaye-shaye ne suka sanya ta yi wa Gabon haka, inda dalilin neman kare kai da Gabon ta yi ne ta fitar da wasu bayanai na hirarraki tsakaninta da Amal, inda a nan aka gano yadda Amal take neman taimakon kudi a wurin Gabon saboda matsalar rashin lafiyarta ko ta mahaifiyarta.

A cikin bayanan da Gabon ta fitar ne ma aka gano yadda Amal take cusa kanta a wurin Gabon, inda idan Amal ta yi wa Gabon magana a Instagram ba ta amsa ba sai ta shiga damuwa.

Sai dai duk da wadannan bayanai jama’a sun ci gaba da cece-kuce a kai, har wadansu suka bayyana Amal ba ta ambaci sunan Gabon a cikin bayaninta na zargin madigo da ta fitar a shafinta na Instagram ba.

Al’amarin ya kara dagulewa ne bayan da lauyoyi 12 suka nemi kwato wa Amal hakkinta na cin zarafinta da suke zargin Gabon ta yi.

Sai dai ana cikin hakan ne sai jaridar Leadership A Yau ta ranar Asabar 13 ga Afrilun bana ta fitar da labari mai taken “Amina Amal Ta Kwanta Jinya Bayan Dukan Da Hadiza Gabon Ta Yi Mata.”

Jaridar ta ce, majiyar da ta yi magana da ita ta ce ana zargin har sai da (’yan tawagar Gabon) suka danne ta (Amal) suka dura mata kayan maye, don ta fadi abin da suke son ta furta a bidiyon da Gabon din ta dauke ta lokacin dukan.

Jaridar ta kara da cewa Amal ta bar Kaduna, saboda hadarin da rayuwarta ke ciki bisa hasashen za a iya daukar nauyin ’yan ta’adda su sake kai mata hari.

Jaridar ta rawaito jim kadan bayan Amal ta bar Kaduna ta kwanta jinya sakamakon barazanar da ta fuskanta, inda likitoci suka yi kokarin ceto rayuwarta saboda ana kyautata zaton cewa lamarin ya haifar mata da ciwo a zuciyarta.

Labarin na Leadership A Yau bai yi wa wata kungiya mai goyon bayan jaruma Gabon dadi ba, inda suka zargi jaridar da kara rura wutar rikici a tsakanin gwanarsu da kuma Amina Amal.

Kungiyar mai suna Team Adizatou Gabon cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun shugabarta, Farida Mafara, ta yi zargin cewa labarin da jaridar ta fitar a ranar 13 ga Afrilu, 2019 mai taken “Amina Amal Ta Kwanta Jinya Bayan Dukan Da Hadiza Gabon Ta Yi Mata” ba gaskiya ba ne, an kuma rubuta shi ne don wata mummunar manufa.

Kungiyar ta ce a labarin an rubuta Amina Amal ta kwanta jinya, amma babu sunan asibitin da ta kwanta jinyar, ba a bayyana ko a gida ta kwanta jinyar ba, an kuma ce jarumar ta bar gari don gudun kada a kai mata farmaki.

Ta kara da cewa hakan ya nuna an yi tufka da warwara a labarin, saboda an ce jarumar ta kwanta jinya, kuma an ce ta gudu. Ta yaya wanda ke kwance jinya zai gudu? Sai dai ko a gudu da shi ko?

“Bincikenmu ya nuna Amal ba ta kwanta rashin lafiya ba, hasali ma tana wani otal da ke Kano tana shakatawa abinta. Sannan a-kai-a-kai tana ta dora hotuna a shafinta na Instagram, wanda ke kara shaida lafiyarta kalau,” inji Farida.

Kungiyar ta yi zargin cewa jaridar ta rubuta labarin ne saboda jaruma Gabon ta taba samun sabani ne da Editan jaridar, inda a yanzu yake ganin lokaci ne da zai yi amfani da damarsa wajen bakanta wa gwanarsu.

“Abin da ya faru shi ne a shekarun baya, Editan jaridar ya taba samun Hadiza Gabon ya ce su hada kudi su yi fim, inda ta ba shi Naira miliyan 2 da dubu 800, an yi fim din amma bai dawo mata da kudinta ba,

“Jarumar ta kai kararsa gaban Kungiyar ’Yan fim ta MOPPAN, inda aka zauna, a karshe ya ba ta Naira miliyan 2 da kyar, inda ta yafe masa sauran Naira dubu 800, amma duk da haka daga lokacin ya kullaci jarumar, yanzu kuma yake ganin ya samu damar bakanta mata,” inji Farida.

Farida ta kara da cewa a yanzu haka abin yana damun jaruma Hadiza Gabon, tana jin ina ma wannan hargitsi ba a yi shi ba. Kuma ya kamata a yi mata uzuri saboda dan Adam tara yake bai cika goma ba.

Ta ce, “Fatanmu shi ne a sasanta ta hanyar da ya fi alheri ga masana’antar, don haka muna kira ga jaridar Leadership A Yau ta kasance jakadiyar zaman lafiya ba jakadiyar kara rura wutar rikici ba.”

Sai dai da Aminiya ta tuntubi Editan Jaridar Leadership A Yau, Nasir S. Gwangwazo, ya ce ba ya  da hannu wajen rubuta labarin.

Ya ce, “Ni Editan jaridar ne daga Litinin zuwa Juma’a, ba ni da iko a kan labaran da za su fita ranar Asabar da Lahadi, don haka ba ni da hannu wajen rubuta labarin.

“Tabbas na yi huldar kasuwanci da Gabon amma ban kullace ta ba, babu kuma wata riba da zan ci a kan labarin da aka buga a Leadership domin ban ma taba ganin Amina Amal ba, ballantana a ce ina goyon bayanta,” inji shi.

Ya ce, idan ma abin da aka zarge shi na kasa biyan Gabon ragowar Naira dubu 800 gaskiya ne, sannan kuma ta yafe masa kudin da take binsa, kamata ya yi ya zama dan gidanta, ba wanda zai kullace ta ba.

Aminiya ta kira Amina Amal ta waya sau 12, ta tura mata sako kan batun ko ta kwanta jinya dalilin dukan da ake zargi an yi mata, amma jarumar ba ta amsa waya ba, ba ta kuma ba da amsar sakon da aka tura mata ba.

Da aka tuntubi jaruma Gabon ko ta sa an yi wa Amal dukan kawo wuka har ta kwanta jinya, sai ta ce a tuntubi Manajanta kuma mai magana da yawunta, wato Ibrahim Birniwa.

Birniwa ya ce abubuwan da aka rubuta a labarin kirkirarru ne, “An fake ne a karkashin damar da aka ba dan jarida ta boye majiyarsa aka yi mugayen bayanan da babu su.”

Ya ce, mafi muni shi ne inda aka ce wai Hadiza ta yi hayar ’yan ta’adda domin su kashe Amal, ai ka ga wannan daga ji zance ne marar tushe, kuma ko a cikin Kannywood din mutane suna ta Allah wadai da wannan rubutu da aka yi mai cike da kiyayya.

Ya ce, “A labarin Leadership ba su tuntubi bangaren Hadiza Gabon ba, wanda dole haka ya kamata a yi a bisa tsarin aikin jarida, sannan ba a ji kuma a cikin rubutun an ce an yi kokarin tuntubar bangaren Hadiza ba. To ka ga wannan kawai wani yunkuri ne na shafa wa Hadiza kashin kaji da nufin jawo mata tsana daga jama’a.”

“Alhamdulillahi mutane sun sani Hadiza mace ce mai kirki ba za ta taba yin tunanin sa a kashe wani ba,’’ inji Birniwa.

Sai dai rikicin ya sake kazanta ne bayan da Amal ta kai Gabon kara kotu, inda ta bukaci ta ba ta hakuri a manyan jaridu biyu na kasar nan, sannan ta biya ta diyyar Naira miliyan 50 saboda zargin cin zarafinta da azabtar da ita.

A yanzu dai abin jira a gani shi ne ko kwamitin zai sasanta bangarorin biyu ba tare da an kai ga fara zaman kotu ba, tun da har zuwa lokacin hada wannan labarin ba a sanya ranar fara sauraren karar ba.