✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin Zakka ya horar da mata a Gombe

A ranar Lahadi  da ta gabata ce Kwamitin Zakkah da Wakafi na Jihar Gombe ya gudanar da taro karo na biyu domin yaye wadansu daga…

A ranar Lahadi  da ta gabata ce Kwamitin Zakkah da Wakafi na Jihar Gombe ya gudanar da taro karo na biyu domin yaye wadansu daga cikin mutanen da ya ba horo kan sanna’o’in hannu tare da ba su tallafin jari da nufin taimaka musu wajen yin sana’o’i a gidajensu.

A bara ce kwamitin ya fara gudanar da wannan taro, inda a wannan karon ya ba mata 51 Naira dubu goma kowacensu.

An samar da kwamitin ne da nufin tallafa wa al’ummar Musulmi marasa galihu da kayayyaki da abubuwan da za su taimaka musu wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum da nufin rage talauci a tsakanin al’ummar Musulmin jihar.

A jawabin Shugaban Kwamitin, Malam Abdullahi Abubakar Lamido ya yi bayanin manufofin kafa kwamitin ne da ayyukansu.

Shugaban Taron, Sheikh Mohammad Bello Doma ya yi bayani kan yadda Zakkah da Wakafi ke da matukar muhimmanci.

Dokta Mansur Isah Yalwa daga Jihar Bauchi da ya samu hallartar taron, ya bayyana yadda zakkah take a Musulunci da kuma yadda take da amfani a tsakanin mutum da mutum.

Malam Mahmud Ibrahim Shira kuwa cewa ya yi idan Allah Ya ba mutum dukiya to sai dai idan bai gadama ba ne wajen samu rahamar Allah.

Sauran baki a wajen taron sun hada da Alhaji Yarima Abdullahi da Dokta Umar Garba Dokaji da Maryam Yaya Mohammad wadda aka fi sani da Maman Biyu da A’isha Abubakar da sauransu.