✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin Zakka ya tallafa wa mabukata a Jihar Abiya

Kwamitin Zakka da Wakafi ta Jihar Abiya ya tallafa wa wadansu daga cikin Musulmin jihar da kekunan dinki da injinan markade da kuma kudi. Kudaden…

Kwamitin Zakka da Wakafi ta Jihar Abiya ya tallafa wa wadansu daga cikin Musulmin jihar da kekunan dinki da injinan markade da kuma kudi.

Kudaden sun kama daga Naira dubu 25 zuwa dubu 65 domin su dogara da kansu, wajen yin sana’a. Da yake raba kayayyakin a Umu’ahiya, Shugaban Kwamitin Malam Sulaiman Olugunju ya ce bayar da zakka na daya daga cikin shika-shikan Musulunci haka kuma tausayi da taimako dabi’a ce ta Musulunci.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, jami’in gudanar da kwamitin, Alhaji Suleiman Ukandu  ya nanata muhimmancin fitar da Zakka, inda ya ce “Akalla duk mutumin da ya mallaki tsabar kudi da suka kai Naira miliyan daya da rabi, kuma suka shekara ya wajaba ya fitar da Zakka.”

Alhaji Yaro Danladi, Sarkin Hausawa da Fulanin Umuahiya, godiya ya yi ga kwamitin a madadin wadanda suka karbi Zakkar.

Uwargida Hauwa Yahaya, daya daga cikin wadanda suka samu Zakkar ta shaida wa Aminiya cewa “Na yi matukar farin ciki da samun wannan tallafi. Na samu abin sana’a da kuma jari.”