✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwana 100 a gadon mulki: Yadda gwamnoni ke tafiyar da mulki ba kwamishinoni

A yau ne gwamnonin kasar nan da aka zaba a bana suka cika kwana 100 a mulki, bayan rantsar da su a ranar 29 ga Mayun…

A yau ne gwamnonin kasar nan da aka zaba a bana suka cika kwana 100 a mulki, bayan rantsar da su a ranar 29 ga Mayun da ya gabata. Sai dai da dama daga cikinsu suna fuskantar kalubale, ida suke  gudanar da harkokin gwamnati ba tare da kwamishinoni ba. Aminiya ta gudanar da bincike kan wadannan jihohi da halin da suke ciki.

A Jihar Nasarawa Gwamna Abdullahi Sule har zuwa shirya rahoto, bai nada kwamishononi ba, duk da cewa mun samu rahoton cewa ya shirya abubuwa da yawa don cika kwana 100 a kan kujerar mulki a matsayinsa na Gwamna.

Abubuwan sun hada da yaye matasa da aka koya wa yin jan bulo don yin gini da kaddamar da gina hanyoyin karkara da gwamnati za ta yi kai-tsaye da sauransu ba tare da ta ba ’yan kwangila ba.

Kwana 100 da suka wuce, a jawabinsa na rantsuwar kama mulki, Gwamnan ya ce burinsa shi ne  sama wa matasa aiki da sana’o’i don magance zaman kashe wando, wanda ke sanya su zama masu aikata munanan ayyuka.

Gwamnan, wanda injiniya ne kuma dan kasuwa ya ce ya kuduri aniyar zamanantar da mabubbugar ruwa da ke garin Farin Ruwa a Karamar Hukumar Wamba don a rika yin yawon shakatawa da yin fina-finai don a samar da kudaden shiga.

Gwamna Sule ya kai ziyarar ba-zata a ma’aikatu da hukumonin gwamnati, wanda haka ya sanya wadansu manyan ma’aikata suka tsallaka ta katanga suna rugawa ofisoshinsu don kada a yi musu sakiyar da babu ruwa. Wannan ya sa washegari,  ma’aikatan gwamnati suka fita aiki kafin karfe 8:00 na safe.

Wani al’amari shi ne yadda ’yan bindiga suka fara addabar jihar, inda Mataimakin Gwamna, Dokta Emmanuel Akabe ya tsallake rijiya da baya, ’yan sanda masu rikiyarsa uku da direbobi biyu suka rasu, sannan aka kama mutum bakwai har sai da suka biya diyya sannan suka kubuta. Hakan ya saya sanya aka kara yawan jami’an taro a manyan hanyoyin jihar.

A Jihar Zamafara ma labarin bai canja ba, domin sabon Gwamna Bello Muhammad Matawalle har zuwa yanzu da ya cika kwana 100 bai kafa Majalisar Zartawa ba.

Kawo yanzu babu wani dalili da ya ba da na rashin nada kwamishinoni a jihar, amma masu fashin bakin siyasa a jihar na ganin cewa jinkirin ba ya rasa nasaba da yadda jam’iyyarsa ta PDP ta samu kanta a mulkin jihar ba tare da kyakkyawan shiri ba.

“Ka san gwamnatin ta Matawalle ta zo ne ba tare da wani shiri ba. Kuma akwai yiwuwar zai duba wasu bangarori na siyasa da suka taimaka wa kafuwar gwannatin tasa. Kuma wadannan bangarori ba ma daga jam’iyyarsa suke ba,” inji wani mai sharhi kan siyasar jihar.

To sai dai Babban Daraktan Yada Labarai na Gwamna Matawalle, Alhaji Yusuf Idris ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu Gwamnan bai fidda wani lokaci da zai nada kwamishinoninsa ba, yana mai cewa har yanzu ba ma a kai jerin sunayen wadanda za a nada ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantacewa ba. Sai dai duk da haka yana da tabbacin cewa za a kafa Majalisar Zartarwar nan ba da dadewa ba.

A Jihar Taraba ma har yanzu Gwamna Darius Ishaku bai nada kwamishinoni ba. Kuma zuwa hada rahoton nan, ba wata sanarwa da Gwamnan ya bayar dangane da wannan lamari.

Sai dai kuma Gwamnan ya sake nada Mista Anthony Jelason a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar da kuma Babban Mai ba shi Shawara ta fuskar Watsa Labarai, Mista Bala Dan Abu.

Shi ma Malam Hassan Mijinyawa, Gwamnnan ya sake nada shi a matsayin Sakataren Watsa Labarai. Amma baya ga wadanan mukamai har zuwa yanzu Gwamnan bai nada kwamishinoni da masu ba shi shawara ba duk da cewa ba sabon shiga ba ne.

Wata majiya ta shaida wa Amimiya cewa shari’ar da ake yi a kan zaben Gwamnan, tsakaninsa da Jam’iyyar APC ne ta hana Gwamna Darius Ishaku nada kwamishinonin. Majiyar ta ce da zarar an kammala wannan shari’ar, in Gwamnan ya samu nasara, zai nada Majalisar Zartarwar Jihar.

A Jihar Filato kuwa, Alhaji Bashir Musan Sati, Sakataren Jam’iyyar APC a jihar, ya bayyana wa Aminiya dalilin da har zuwa wannan lokaci Gwamna Lalong bai nada kwamishinoni ba. Ya ce ba rashin jituwa ko rashin kudi ne ya kawo tsaikon nada sababbin kwamishinoni a Jihar Filato ba.

“Idan ka lura Gwamna Lalong ya fara maganar nada kwamishinoninsa, domin a ranar Litinin da ta gabata ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar da sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati. Kuma a wajen rantsar da wadannan shugabanni, Gwamna ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa ya kammala rubuta sunayen sababbin kwamishinoninsa. Ya tabbatar wa jama’a cewa ba don Shugaban Majalisar Dokokin Jihar ya yi tafiya ba, da ya mika sunayen kwamishinonin don tantancewa. Saboda haka wannan magana ta sababbin kwamishinoni a Jihar Filato, tana kan hanya” inji shi.

Da aka tambaye shi ko ba ya ganin cewa tsaikon nada kwamishinoni ya kawo rashin tafiyar harkokin gwamnati a jihar, sai ya amsa da cewa: “Wannan  bai kawo tsaikon komai kan tafiyar da harkokin gwamnati ba, domin abin da yake akwai shi ne kwamishinoni shugabanni ne masu kai wa Gwamna rahoto kuma su ne suke kula da ma’aikatun da aka tura su. Ai babban jagoran tafiyar kowace ma’aikata shi ne Babban Sakatare kuma kowace ma’aikata akwai Babban Sakatare kuma dukkan ma’aikatun Jihar Filato, manyan sakatarorinsu suna gudanar da ayyukansu.”

A Jihar Bauchi kuwa, an ce rikicin shugabancin Majalisar Dokoki da zakulo kwararru da bai wa masu ruwa-da-tsaki a kananan hukumomi hakkinsu a matsayin dalilan da suka jawo rashin nada kwamishinonin a jihar.

Tsohon Kwamishinan Shari’a na Jihar, Barista Mukhtar Abubakar Othman da Kakakin Jam’iyyar PDP Alhaji Yayanuwa Zainabari ne suka bayyana haka a zantawar da suka yi da wakilnmu a Bauchi.

Mukhtar ya ce “Jinkirin da aka samu na daga rikicin majalisa ya sa haka, daga bisani bayan an daidaita rikicin majalisar sai majalisar ta tafi hutu. Amma kafin su tafi hutu Gwamna ya riga ya mika sunayen mutum 20 da yake so ya nada su kwamishinoni ga majalisar.”

Ya ce doka ba ta iyakance lokacin da aka ce tilas sai Gwamna ya nada Majalisar Zartarwa ba.  Duk lokacin da aka nada su daidai ne.

Dangane da ayyukan biliyoyin Naira da Gwamnan ya yi ta bayarwa ba tare da amincewar Majalisar Zartarwa ba kuwa, ya ce, “Babu wata doka da ta ce tilas sai Gwamna ya nada Majalisar Zartarwarsa kafin ya ba da ayyukan da suke bukatar kulawar gaggawa.

“Yanzu idan aka samu barkewar annoba, shi ke nan Gwamna ba zai dauki mataki a yi maganin abin ba, sai a ce sai ya nada Majalisar Zartarwa, rayuwar jama’a ta shiga cikin wani irin yanayi? Ka ga ba zai yiwu ba, duk ayyukan hanyoyin nan da Gwamna ya bayar da sauran ayyukan da yake yi, al’ummar Jihar Bauchi na bukatarsu ne cikin gaggawa, shi ya sa aka yi haka kuma bai saba wa doka ba. Gwamna yana da dama ya ba da izini a yi aiki duk lokacin da Majalisar Zartaswa ta zauna kuma a bayyana irin umarnin da Gwamna ya bayar da dalilan yin haka; su ma kuma a samu amincewarsu don komai ya tafi daidai,” inji shi.

Kakakin Jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi, Alhaji Yayanuwa Zainabari ya ce “Jihar Bauchi ta sha wahala a shekara hudu da suka wuce wajen Gwamnatin APC. Tunda mun yi alkawarin za mu yi wa al’ummar jihar aiki, tilas a samo mutane kwararru a fagagen da suka kware kuma a nemo nagartattun mutane da ba za su bai wa gwamnati kunya ba, a kuma samu mutane masu dattako da kishin jama’arsu da kishin ci gaban Jihar Bauchi. Bayan an samo su nan ma sai jami’an tsaro sun tantance su, Majalisar Jihar Bauchi ma ta tantance su tukuna; in kowa ya amince sai a nada su, Gwamna ya rantsar da su.”

A Jihar Katsina kuwa, Gwamnan Aminu Bello Masari, Kwamishina daya ne rak ya nada, kuma da Aminiya ta tunutube kan sauran sai ya ce yanzu babban abin da ke gabansa shi ne na samar da zaman lafiya tukunna.

Shi kuma Gwamnan Ribas Neysom Wike ya nada kwamishinoni biyu ne. Sai  Gwamna Samul Ortom na Jihar Binuwai da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas da suka tura sunayen wadanda suka zabo a matsayin kwamishinoni  ga majalisun jihohinsu don su samu amincewarsu.

A Jihohin Neja da Kebbi da Ogun da Imo da Kwara da Yobe da Enugu da Borno da Adamawa da kuma Kano da Jigawa da Kuros Riba da Ogun da Delta da kuma Ebonyi, abin da aka fi gani shi ne, gwamnoni suna nada sakatarori da shugabannin ma’aikatan gidan gwamnati da kuma masu magana da yawunsu. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana cewa ya jinkirta zaben kwamishinoninsa ne saboda yana son ya zabo sahihan mutanen da zai yi aiki da su.

Shi kuma Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar ba tare da wata sanarwa a hukumance ba an ce Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa Abdulkadiri Fanini ya ci gaba da aikinsa.

Ana ganin babban dalilin da ya sanya mafi yawan gwamnonin suka ksa nada kwamsihinoninsu ba zai rasa nasaba da yadda ba su iya zama a  jihohinsu balle su yi aikin zabo kwamishinonin. Gwamnonin sun gwammace su tare a Abuja su rashe na tsawon makonni don neman gindin zama a fadar Shugaban Kasa kuma kuma kulla wasu harkokinsu na siyasa inda suke kauce wa yin ayyukan da jama’arsu suka zabe su su yi musu.

Shin  me dokar kasa ta ce game da samar da Majalisar Zartarwa a jihohi? Lauya mai zaman kansa a Jihar Gombe, Barista Abdullahi Muhammad Inuwa (Tamatuwa) ya  ce babu dokar da ta kayyade lokacin da Gwamna zai nada kwamishinoninsa amma akwai dokar da ta ce ya nada, don haka ganin damar Gwamna ne ya nada su a lokacin da ya ga ya dace.

Barista ya ce Gwamna zai je ne ya zauna ya yi nazari, ya duba ya ga wadanda suka cancanta, ya kuma amince da su a lokacin da ya so; tunda ba a kayyade masa wa’adi ba.

Ya kara da cewa sashi na 192 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba Gwamna dama ya nada kwamishinonin da za su masa wakilci nagari a ma’aikatun gwamnati daban-daban gwargwadon yadda yake son su yi masa aiki.

“Ka’ida dai ita ce, a bi tsari kamar yadda dokar kasa ta nuna a sashi na 14 sakin layi na 4 na tsarin mulki, wanda ya shafi daidaito (National Character), inda aka ce kada ya nuna bambanci ga jama’a na bangaranci ko addini ko kabila wajen nada kwamishinonin, kada a tara su da yawa a bangare guda, a hana wani bangare,” inji lauyan.

Ya kara da cewa ba laifi ba ne kai-tsaye amma zai iya zama laifi a fakaice idan Gwamna ya dauki lokaci bai nada kwamishinoni ba, saboda duk abin da doka ta ce a yi, koda ba a kayyade lokaci ba yana da kyau a yi shi a kan lokaci.