✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwana 9 surikin Buhari na hannun masu garkuwa da mutane

Yau kwana tara kenan surikin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wato Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, wanda masu garkuwa da mutane suka kama shi…

Yau kwana tara kenan surikin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wato Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, wanda masu garkuwa da mutane suka kama shi kuma har yau ba su sako shi ba, yana daya daga cikin manyan masarautar Daura. An yi garkuwa da shi lokacin da yake gidansa a ranar 1 ga watan Mayu 2019.

Majiyarmu ta gano cewa, Magajin Garin Daura yana auran `yar dan uwan Buhari, wato  Hajiya Bilki, har yanzu ba a kubutar da shi ba daga hannu masu garkuwa da mutanen, a jiya Alhamis ne shugaba Buhari ya gana da hafsoshin tsaron kasar.

Bayan ganawar shugaba Buhari da hafsoshin tsaron Najeriya, Babban Hafsan rundunar sojin ruwan Najeriya, Riya Admiral Ibok Ekwe Ibas, ya bayyana cewa an kama manyan da suke da hannu wajen yin garkuwa da Alhaji Musa Umar Uba.