Kwana 407 na Buhari a kasashen waje

Shugaba Buhari tare da Sarki Salman, yayin ziyarar aiki a Saudiyya
Shugaba Buhari tare da Sarki Salman, yayin ziyarar aiki a Saudiyya
  • Kwanaki 242 a Ingila, ya yi tafiye-tafiye sau 79 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, zai zarce zuwa Landan na kasar Ingila bayan kammala taron tattalin arziki a kasar Saudiyya domin fara ziyarar kashin kansa ta kwana 15 daga gobe Asabar.

Shugaban wanda ya bar Najeriya a ranar Litinin da ta gabata domin ziyarar aiki a birnin Riyadh na Saudiyya don halartar taron zuba jari a Afrika karo na uku a birnin; inda zai shafe kwanaki biyar zuwa gobe kafin ya ya wuce Birtaniya.

Kakakin Shugaban Kasa Femi Adesina, ya ce a wata sanarwa ana sa ran Shugaba Buhari ya dawo Najeriya daga Birtaniya a ranar 17 ga watan nan.

Kakakin ya ce a Saudiyyar, Shugaban zai yi wata ganawar bayan-fage da Sarki Salman da kuma Sarki Abdallah II na Jordan.

A ranar Larabar makon jiya, Shugaba Buhari ya halarci wani babban taro a Rasha kan makomar Afirka da yadda zuba jari da kasuwanci za su kawo sauyi mai kyau a nahiyar. Tattaunawar ta hada da shugabannin kasashen Kenya da Kongo Brazabille da kuma Burkina Faso.

ADVERTISEMENT

Shugaban ya ziyarci Saudiyya sau biyu a watan Mayun bana  kawai. Na farko ya sanya kafarsa a Saudiyyar tsakanin ranakun 16 zuwa 21 ga wata, domin yin Umra. Sai na biyu, sa’o’i kalilan bayan rantsar da shi ya sabi jakarsa zuwa kasar ranar 30 ga Mayu don halartar wani taron koli karo na 14 na Kungiyar Hada kan Kasashen  Musulmi, wanda Sarki Salman bin Abdulaziz ya dauki bakunci. Ya komo kasar nan a ranar 2 ga watan Yuni.

Fadar Shugaban Kasar ta bayyana cewa Shugaban a wannan karon zai shafe kwana 15 a birnin Landan. Idan za a iya tunawa, a baya Shugaban ya shafe kwanaki 227 a Ingila, wanda hakan zai sanya ya shafe kwanaki 242 a kasar kawai tun hawansa mulki.

Wani lokaci a farkon  bana, Buhari ya kasance a Birtaniya na kwanaki 10 domin ziyarar kashin kansa, inda ya shiga kasar ranar 25 ga Afrilu zuwa 5 ga watan Mayu.

Binciken Aminiya ya nuna yadda Shugaba Buharin ya ziyarci Ingila domin hutunsa na shekara, daga ranar 9 zuwa 21 ga watan Afrilun 2018. A watan Mayun bara kuma ya dan tsaya na wani lokaci domin wasu dalilai. Tsakanin 8 zuwa 11 ga watan Mayun, Shugaban ya kuma kasance a Ingila. Harwa yau ya ziyarci kasar a ranar 3 zuwa 18 ga watan Agustan bara.

A farkon 2017 Shugaba Buharin ya je jinya daga ranar 19 ga Janairu zuwa 10 ga watan Maris. Aminiya ta bayar da rahoton  cewaa lokacin Shugaban ya mika ragamar iko ga mataimakinsa, Yemi Osinbajo. Wata biyu kawai bayan komawarsa gida, ya sake ficewa zuwa Ingila, inda ya shafe kwanaki 104, daga 8 ga watan Mayu zuwa 19 ga watan Agustan 2017.

Buhari ya kasance a Birtaniya tsakanin 5 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2016, domin hutu. A ranakun 13 zuwa 15 na shekarar ya kasance a Birtaniyar domin taron koli kan yaki da cin hanci. Har wa yau, a shekarar 2016, Shugaba Buhari ya kuma ziyarci Birtaniyar domin neman maganin ciwon kunne.

Buhari na guje wa nauyin da ke kansa – Daraktan CSJ

Babban Daraktan Cibiyar Tabbatar da Adalci a Zamantakewa (CSJ), Eze Onyekpere, wanda lauya ne ya ce Shugaba  Buhari yana kaurace wa nauyin da ya rataya a wuyansa ne, shi ya sa yake irin wadannan tafiye-tafiye.

Ya ce, ’yan Najeriya ba su tursasa masa lallai ya zama Shugaban Kasa ba, bil hasali ma ya barje gumi sosai domin darewa karagar mulki, sa’annan ya nemi wa’adi na biyu, don haka ba ya da hujjar yi wa kasar rikon sakainar kashi.

Ya ce ba zai yiwu a ce Shugaban yana ta gantali tsakanin kasashen duniya ba; alhali yana barin kasar cikin wahala.

“Lallai ne ya zauna a gida domin ya shawo kan matsalar tsaro da ke kara gauni tare da sauran matsalolin da ya sha rantsuwar tunkararsu gaba gadi,” inji shi.

Tafiye-tafiyen Buhari abin dariya ne – Shugaban GGT

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Samar da Mulki Nagari a Najeriya (GGT), Mista Tunde Salman, ya shawarci Shugaban da ya zama mai tantancewa ko zabar gayyatar da kasashen duniya ke  yi masa.

“Ya kamata ya rika tura Ministan Harkokin Waje domin halartar wasu daga cikin wadannan tarurruka da ke neman zama abin takaici ko na ban dariya. Shugaban Najeriyar bai kamata yana halartar kananan tarurruka nan da can ba, domin daga kimar kasar a idon duniya,” inji Salman.

Bai dace ga Shugaban Kasa ba – Yakudima

Da yake mayar da martani game da halartar tarurrukan kasashe barkatai da Shugaban yake yi, wani jigon da aka kafa Jam’iyyar PDP da shi, Alhaji Aminu Yakudima ya ce tafiye-tafiyen Shugaba Buhari sam ba su dace da Shugaban Kasa ba.

“Mun damu da tafiye-tafiyen Shugaba Muhammadu Buhari. Tattalin arziki na tangal-tangal, kuma akwai yiwuwar ya durkushe idan dai har ba a dauki mataki ba.

“Don haka, muna bukatar Shugaban ya zauna wuri guda domin zaburar da wasu batutuwan. Sanannen abu ne cewa Shugaba Buhari ya shafe shekara guda da wata biyu ba ya cikin Najeriya. Hakan ya sanya shi daukar kambin Shugaban Kasar da ya fi tsara a fagen tafiye-tafiye, tun samun ’yancin kasar nan.

“Muna bukatar ya zauna cikin gida, domin magance matsalolin kasar nan. Babu hujjar ya zama kullum yawo yake yi a kowane lokaci. Akwai bukatar lallai a gyara haka,” inji shi.

Sai dai Kakakin Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce jam’iyyar za ta fitar da matsayarta game da tafiye-tafiyen Shugaba Buhari nan gaba.

Daidai ne kuma suna kan turbar muradun kasa – Bako

Sai dai a nasa martanin, wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Dokta Abbati Bako, ya ce Shugaban yana tafiye-tafiyen ne da zimmar jawo hankalin masu zuba jari cikin kasar nan.

“Maganar gaskiya, daya daga cikin ginshikan dunkulewar duniya waje guda shi ne shiga siyasa tare da harkokin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa. Idan ka lura za ka ga a yanzu tattalin arzikin duniya ya dogara ne kan hadewar kasashen duniyar waje guda. Don haka, dalilin yawaitar tafiye-tafiyen Buhari zuwa kasashen duniya shi ne jawo hankalin masu zuba jari zuwa kasar nan domin zuba gagarumin jari a fannin tattalin arziki. Najeriya ce babbar kasar Afirka, mai mutane fiye da miliyan 200.

“Don haka, a ganina tafiye-tafiyen Shugaban Kasar za su jawo samar da ayyuka ga dimbin jama’a da zaburar da komadar tattalin arziki da kuma taka birki ga hauhawar farashi a Najeriya,” inji shi, a wani sakon tes da ya aike wa daya daga cikin wakilanmu.

Jama’a da dama dai suna korafin cewa har yanzu ba su gani a kasa ba game da batun zuba jari a kasar nan, ta dalilin tafiye-tafiyen Shugaba Buhari.

Sannan sun ce kasar Ingila da ya fi zuwa ba yana zuwa ne don neman masu zuba jari ba, yana zuwa ne don kashin kansa, don haka ko ya je babu wata riba da kasar nan za ta samu.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya