✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso ya dauki nauyin karatun dalibai 242 zuwa Indiya

Gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyin karatun dalibai 242 da suka kammala karatun jami’a zuwa kasar Indiya don yin karatun digiri na biyu. Gidauniyar ta ce,…

Gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyin karatun dalibai 242 da suka kammala karatun jami’a zuwa kasar Indiya don yin karatun digiri na biyu.

Gidauniyar ta ce, ta nada shirin daukar adadin karatun dalibai 370 a wannan shekarar.

Shugaban gidauniyar Kwankwasiyya na kasa Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce daukar wannan nauyin karagtun daliban na cikin rukunin farko da aka tsara don daukar dalibai 242 cikin 370, don fita da su kasar waje karo karatu.

Lokacin da daliban ke shirin tafiya

Dakta Kwankwaso, ya ce takwas cikin dalibai 242 mne kawai zasu yi karatun digiri na biyu a tsangayar koyon Larabci da ilimin addinin musulunci a Sudan, sauran za a tura su jami’o’in kasar Indiya ne.