✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso ya raba motoci da kudi ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars

Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso naJjihar Kano, ya raba kudi tare da sababbin motoci kirar Toyota Picanto ga kowane daga cikin ’yan wasan kwallon kafa na…

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar KanoGwamna Rabiu Musa Kwankwaso naJjihar Kano, ya raba kudi tare da sababbin motoci kirar Toyota Picanto ga kowane daga cikin ’yan wasan kwallon kafa na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, tare da baiwa kowanensu Naira dubu 500.  Su kuma jami’an kulob din na Pillars, kowanensu ya samu Naira dubu 750.
Haka nan gwamnan ya bayar da kyautar kudi ga wadansu karin kungiyoyin kwallo da suka hada da ta kwallon Kwando ta Kano Pillars wadda ta samu kyautar  Naira dubu 250 yayin da jami’ansu suka tashi da Naira dubu 150 kowanensu.
Su kuwa ’yan wasan kungiyar kwallon guragu, sun samu kyautar Naira dubu 500 ne kowane.   Sai kuma wasu kananan kungiyoyin wasan kwallon kafa su 13 da suka samu kyautar Naira dubu 500 ga kowace kungiya.
A jawabinsa a wajen taron raba kyaututtukan a zauren taro na fadar gwamnatin jihar Kano, Gwamna Kwankwaso ya ce taron “ya nuna wani karin mataki na ci gaba a cikin gwmanatinmu, wacce a halin yanzu ta cika shekaru biyu da hawanta kan gado”.
Ya kuma ce an baiwa ’yan wasan na Pillars kyautar ne a sboda bajintar da suka nuna musamman wajen daukaka suna da martabar Kano,a wuraremn wasanni daban daban da suka kara a shekarar bara.
Gwamnan ya kara da cewa saboda muhimmancin da harkokin wasanni ke da shi a tsakanin matasa ya sa gwamnatin jihar gina Kwalejin koyon harkokin wasanni a garin Karfi tare da kokarin samar da cibiyar samar da harkokin wasanni irin ta zamani a kofar Na’isa da ke cikin  birnin Jihar.
Ya yi alkawarin cigaba da bayar da gagarumar gudunmawa don ganin Jihar ta cigaba da yin zarra a dukkan bangarorin wasanni a ciki da wajen kasar nan.