✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwantaina ta rufta kan kananan motoci a Legas

Dazun nan kenan wata kwantaina ta ruftowa wasu kananan motoci a kan hanyar Warf wato babbar tashar jiragen ruwa ta kasa da ke Apapa a…

Dazun nan kenan wata kwantaina ta ruftowa wasu kananan motoci a kan hanyar Warf wato babbar tashar jiragen ruwa ta kasa da ke Apapa a Legas.

Hanyar Warf da ke Apapa a Legas hanya ce mai yawan tarin cunkoson ababan hawa inda ko a bayabayan nan Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin ko ta kwana domin magance cunkoson manyyan motocin a hanyar, haka zalika gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanya rege cinkoson ababan hawa a wannan hanya a cikin daya daga cikin mahimman ayyukan da zai baiwa fifiko lamarin da ya sanya shi ziyartar wajen jim kadan da kama aiki a matsayin sa na gwamnan jihar.

A jihar Legas akan sami yawaitar faduwar kwantaina da a lokuta dama ke fadawa kan kananan motoci inda akan sami asarar rai.