Kwamandan rundunar kwastam a jihohin Oyo da Osun, Kwanturola Richard Oteri ya ce a cikin watanni 3 rundunarsa ta yi nasarar kama wasu kayayyakin da suka hada da buhunan shinkafa 3,263 da aka kiyasta ta kai Naira miliyan 49 da dubu dari 3 da kuma kanana da manyan motocin bas-bas na tokunbo, wadanda aka cunkusa tayoyin mota da turamen yaduka iri-iri da takalma da galan-galan na man gyada masu yawa da aka kiyasta kudinsu a kan fiye da Naira miliyan 300 da 15.
Da yake nuna wa ’yan jarida kayayyakin a ofishinsa a Ibadan, Kwanturola Richard Oteri ya nuna a kame-kame 181 da jami’ansa suka yi a garuruwan Shaki da Kishi da Okeho duk a kusa da kan iyakar Najeriya da Benin da Bakatari da ke tsohuwar hanyar Ibadan zuwa Abeokuta.
Ya ce an kama mutum uku da ake zargin suna da hannu a harkar fasa kwauri.
Kwanturola Oteri ya bayyana cewa shirin wayar da kan jama’a kan muhimmancin biyan kudaden harajin shigowa da motoci cikin kasa ya yi armashi fiye da bara, domin a tsakanin watan Afrilu zuwa Yuli na bara an samu motoci guda 399 da aka biya musu kudaden shigo da su cikin kasa, wanda a daidai wannan lokaci na bana, aka samu motoci 636 da aka biya wa harajin da ya rubanya na bara da kashi 50 cikin dari..
Kwastam sun bayyana matsayin kamen da su ka yi a Jihar Oyo
Kwamandan rundunar kwastam a jihohin Oyo da Osun, Kwanturola Richard Oteri ya ce a cikin watanni 3 rundunarsa ta yi nasarar kama wasu kayayyakin da…