✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam sun nemi sarakuna su yi wa talakawa bayanin illar fasa kwauri

Kwamandan rundunar kwastam na jihohin Oyo da Osun, Kwanturola Richard Oteri ya roki sarakuna da shugabannin al’umma su ci gaba da wayar da kan jama’a…

Kwamandan rundunar kwastam na jihohin Oyo da Osun, Kwanturola Richard Oteri ya roki sarakuna da shugabannin al’umma su ci gaba da wayar da kan jama’a a game da illar fasa-kwauri da irin barazanar da yake haifarwa ga harkokin tsaron kasa.
Ya ce, “Duk masu sha’awar shiga hada-hadar kasuwanci da kasashen ketare su zo mu yi musu bayani, mu ba su muhimman shawarwari don bunkasar kasuwancinsu, amma fasa-kwauri na janyo hasarar dukiya da yi wa tattalin arziki zagon kasa.”
Kwanturola Oteri, ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis a ofishinsa da ke Ibadan yayin da yake yi wa taron ’yan jarida bayanin nasarorin da rundunar ta samu a cikin watanni 4 na farkon shekarar 2013.
Ya ce kudaden haraji da rundunar ta tara a wannan lokaci ya haura na bara da karin kashi 17 na jimlar kudin. Daga cikin kayayyakin da rundunar ta yi nasarar kamawa, akwai buhunan shinkafa guda 2,716; da wasu kananan motoci da jif-jif guda 28; da katon katon na yankakkun kaji guda 2,500; da wata babbar mota dauke da kwalayen sababbin takalma guda 700; da wata motar bas da aka cika ta da haramtattun suturu daban-daban; da tayoyon mota guda 521; da wata motar tirela da aka yi mata lodin buhuna 600 na abincin dabbobi; duk wadanda kwanturolan ya nuna wa ’yan jarida. Daga cikin kayayyakin har da kwalayen hasasan da rundunar da kama.
Kwanturola Richard ya ce, “Rundunar kwastam ta kasa, a karkashin Kwanturola-Janar Abdullahi Dikko Inde, ta wadata mu da kayan aiki, shi ya sa muke gudanar da aiki wajen durkusar da fasa-kwauri da samar da kudaden shiga aljihun gwamnati. Akwai bukatar jama’a, musamman wadanda ke kusa da iyakokin kasa su bayar da tasu gudunmawar tona masu fasa-kwauri da sababbin dabarun shigowa da kayayyaki ta haramtacciyar hanya.