Da Dumi Dumi

Kwastam ta kama kwantainoni 32 na lalatacciyar shinkafa

Hukumar Kwastam ta kama wasu kwantainoni 32 cike da buhunan lalatacciyar shinkafa. An kama  kwantainoni ne a daidai lokaci da kokarin shigowa da su kasuwannin Najeriya.

Kamar yadda Shugaban Hukumar Kanar Hamid Ali ya bayyana a lokacin da yake duba kwantainoni ya ce an shigo da shinkafar ce daga kasashen Thailand da kuma China.

Kanar Ali ya ce shinkafar ba ta da kyau duk ta lalace lokacin da ya kamata a ce an yi amfani da  shinkafar ya wuce tuntuni.

Ali ya ci gaba da cewa a cikin kwantainonin an ga sababbin buhuna da aka buga musu sabon hatimi da ranakun kare aiki daban.

“A cikin wadannan buhuna ne nake kyautata zaton za a dura wannan shinkafa domin sayar da ita ga mutane a kasuwanni,” inji shi.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya