✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama motoci 39 masu alamar UNICEF da NNPC

Hukumar Kwastam a jihar Kaduna ta yi nasarar kama wasu motoci 39 wanda ake kokarin shigo da su cikin kasar nan ta barauniyar hanya masu…

Hukumar Kwastam a jihar Kaduna ta yi nasarar kama wasu motoci 39 wanda ake kokarin shigo da su cikin kasar nan ta barauniyar hanya masu dauke da alamar Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da na NNPC.

Shugaban Yaki da Safarar kayayyaki zuwa cikin kasar nan DCC Baba Kura Kolobe,‎ ne ya sanar da hakan a lokacin da yake nuna motocin da sauran kayayyaki da suka kama ga manema labarai a Kaduna.

Ya kuma ce, ‎ma’aikatansu sun yi nasarar kama buhuhunan shinkafa ‘yar waje dubu 5,600 da aka yi kokarin shigowa da su cikin kasarnan.

“Mun kuma kama kayan gwanjo har dubu 1,953 da jarkunan man gyada 1,095 na lita 25. Sai motoci  ‎39 ciki har da wadanda ke dauke da alamun UNICEF da NNPC sai kuma wasu motocin yan Kwatano da muka kama a bakin iyakokin kasar nan,” in ji shi.

Motocin da aka kama masu alamar UNICEF

Ya kuma shawarci jama’a musamman ‘yan kasuwa da su rika bin ka’idoji wajen shigowa da kayayyaki cikin kasar nan inda ya ce, yin hakan zai taimakawa tattalin arzikin kasa da sauransu.

” Muna kare rayukan ‘yan kasa ne domin yawancin kayayyakin da ake shigowa da su musamman shinkafa da Sauran atamfofi da kayan gwanjo na da hatsari ga rayukan jama’a da kuma tattalin arzikin kasar nan.

“Domin ba muna kama mutane bane domin kawai mu cutar da su a’a manufar mu ce mu kare kasar nan, mu kuma bunkasa tattalin arzikin mu wanda hakan yasa dole mu hana shigo da ‎kayayyakin da gwamnati ta haramta shigo da su domin baiwa na gida damar bunkasa,” in ji shi.