✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kame mai safarar kudin bogi tare da barasa mai guba a Ogun

Jami’an Hukumar Kwastam da ke aiki a shiyya ta daya a jihar Ogun, sun yi nasarar kame wani mutum da kudi Naira miliyan biyu da…

Jami’an Hukumar Kwastam da ke aiki a shiyya ta daya a jihar Ogun, sun yi nasarar kame wani mutum da kudi Naira miliyan biyu da dubu dari biyar na jabu, sannan ta kama tarin barasa mai guba wacce wasu wasu batagari keyin safarar ta a kan iyakar kasar nan da ke yankin Idiroko a jihar Ogun.

Da yake wa manema labarai karin haske bisa kamen Kwanturolan Hukumar mai kula da shiyya ta daya a jihar Ogun, Micheal Agbara ya shaida cewa jami’an Hukumar sun kame mutumin wanda ke dauke da kudin jabun a yankin Ihunbi da ke kan hanyar Sango zuwa Idiroko, ya ce mutumin mai suna Samson Odebija, ya shaida cewa wani malamin tsubbu ne ya bashi dakon kudin inda ya nemi ya ketarar masa da su zuwa garin Owode akan ladan aikinsa Naira dubu 5.

Micheal Agbara, ya kara da cewa jami’an Hukumar sun yi nasarar kame durom 40 na sinadarin barasa da masana’antu ke sarrafawa ta itanol, ” Sinadarin barasar wanda ke dauke da tambarin Hukumar kula da kayayyakin abinci da magungunan ta kasa wato NAFDAC an samar da shi ne, domin amfanin masana’antu amma sai masu fasakwabrin ke yin safararsa zuwa garuruwan da ke kan iyaka inda suke surka shi da ruwa suna durawa a kwalabe ana sha a matsayin barasa wannan sinadari ne mai guba da ka iya yin lahani ga lafiyar jama’a.” In ji shi.

Ya ce, jami’an Hukumar da ke yaki da masu fasakwabrin man fetur sun gano maboyar ‘yan fasakwabrin man a yankin Igo-gate a Idiroko, inda suka kame jarkokin man fetur 160 dauke da litar man 25 kowannen su, “Mun kuma bankado dabarun da ‘yan fasakwabrin ke yi na yunkurin su na fitar da man kasashen ketare inda suke gina bututu a gonakin rogo sai su janye man daga babbar motar tanki man su dura su a jarkoki, sai dai jami’anmu a tsaye suke za mu ci gaba da karya lagon su duk da sabbin  dabarun nasu.” In ji shi.

Ko a makon jiya ma Hukumar ta Kwastam a jihar Ogun, ta kame shinkafar fasakwabri da aka sanya ta a jarkoki, aka yi baddakamaninta da manja.

Kudin bogi da aka kama
Jarkokin da ake hada guba da aka kama