✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kame man fetur da aka yi fasakwabrin su a akwatin gawa

Jami’an Hukumar Kwastam da ke aikin akan iyakar Najeriya da kasar Benin sun yi nasarar kame man fetur da aka yi kokarin fasakwabrin su a…

Jami’an Hukumar Kwastam da ke aikin akan iyakar Najeriya da kasar Benin sun yi nasarar kame man fetur da aka yi kokarin fasakwabrin su a cikin akwatun daukar gawa.

Mai magana da yawun Hukumar Kwastam da ke aiki a shiyya ta daya a jihar Ogun Abdullahi Maiwada, ya shaida wa Aminiya cewa jami’an nasu sun kame mota kirar Mazda mai lambar Legas LSD 617 CW dauke da akwatun daukar gawa biyu da aka yi fasakwarin man fetur cike a manyan jarkoki lita 25 guda 13 da kuma jarka mai cin lita 10 guda 6, ” Su na yunkurin fasakwabrin man fetur din ne zuwa makwabtan kasar mu, sun banzatar da motar suka gudu a lokacin da jami’an su suka farmasu.” In ji shi.

Binciken da Aminiya tayi a kan iyakar kasar nan da kasar Benin ta gano cewa, a yanzu ‘yan fasakwabrin sun maida hankalin su ne, wajen fasakwabrin man fetur zuwa kan iyakokin kasar nan dama ƙasashe makwabtan Najeriya tun bayan da gwamnati ta hana kai man fetur zuwa garuruwan da ke da nisan kilomita 20 daga iyakar kasar nan, lamarin da yasa Hukumar Kwastam ke yawan kamen man fetur na fasakwabri a yankin.