Kwastam ta kame tabar wiwi da aka boye a karkashin gawar mutum

Jami’an rundunar Kwastam da ke aiki a kan iyakar Najeriya da Jamhoriyar Benin a Kwatano yankin Same Boda sun yi nasarar kame manyan kunshin tabar wiwi guda 55 da aka boye su a karkashin gawar wani mutum.

Kwamturolar rundunar Kwastam na Same Boda Muhammad Uba, ya shaida wa Aminiya cewa a yankin Owode da ke kan iyakar kasar a Kwatano jami’an su suka tsare motar da ta dauko gawa sai suka nemi su bincike ta, ko da aka bude akwatun gawar sai suka tabbatar gawa ce aka daukko amma a karkashin ta aka boye tarin kunshin tabar wiwin.

Ya ce bugu da kari, rundunar ta kame motar indomi maqare da tabar wiwi da aka yo fasakwabrin ta daga kasar Ghana, kana izuwa yanzu ana ci gaba da bincikar wadanda ake zargi aikata hakan.

 

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya