✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastan na balle shaguna suna kwashe shinkafa a Katsina

Jihar Katsina wadda ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar ta kan iyakokin Kwangwalam da ke yankin Mai’aduwa da Magamar Jibiya da ke yankin Jibiya, wanda…

Jihar Katsina wadda ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar ta kan iyakokin Kwangwalam da ke yankin Mai’aduwa da Magamar Jibiya da ke yankin Jibiya, wanda hakan ya sa rufe kan iyakokin kasar nan da gwamnati ta yi ya shafi shigi da fici da na kayan masarufi da sauransu.

Sai dai Aminiya ta samu rahoton da ke cewa jami’an Kwastam sun fito da wani sabon salon na shiga gari suna balle shaguna cikin dare suna kwashe kayan jama’a hatta a birnin Katsina wanda ba ya kan iyaka.

Wadansu da suka nemi a sakaya sunansu sun shaida wa Aminiya cewa babban hadarin hakan shi ne yadda wadannan jami’ai ba su zuwa sai lokacin da mai shago ya tashi ya rufe shagonsa, inda cikin dare sai su zo shagon su shiga da karfi su kwaso kayan da suke cewa an hana shigo da su, ba  tare da neman mai shagon ba balle ya san halin da ake ciki. Kuma in suka dauki abin da auke so, sukan tafi su bar shagon ba tare da rufewa ba.

“Wannan ba karamin hadari ba ne, domin wadansu za su iya amfani da wannan dama su shiga su dauki duk abin da suke so. Wadansu ma nan cikin shagon suke ajiyar kudinsu, ke nan komai na iya faruwa,” inji daya daga cikinsu.

Aminiya ta samu labarin cewa abu na baya-bayan nan da ya faru shi ne shigar da  ma’aikatabn Kwastam suka yi cikin Babbar Kasuwar Katsina, suka karya kofofin shiga kasuwar bayan karfe 11 na dare suka bude shaguna biyar na wani Alhaji Yahaya ‘Pure Water’ inda suka kwashe buhunan shinkafa sama da 300.

Sun  kuma je Kofar Guga da shagon Alhaji Ashiru Tankuri da misalin karfe 3:00 na dare kamar yadda wani na kusa da wurin ya bayyana.

“Yanzu gwamnati ta fi daukar mataki a kan buhun shinkafa da ran jama’a,” inji wani mutum.

“Wata matsalar ita ce, maimakon su yi amfani da motocinsu, sai suke amfani da motocin farin kaya kirar J5. Kowane mugu ma sai ya yi amfani da damar. Yaya za a yi a tantance?

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa ta Jihar Katsina Alhaji Mujtaba Lamis Gafai ya ce, “Gaskiya ba mu ji dadin wannan mataki da suka dauka ba a kungiyance. Abin da muka sani kuma muka yi yarjejeniya da duk jami’an tsaron da muke da su shi ne, in har suna neman wani ko wani abin da suke zargi, su kira mu a kungiyance kuma mu kai masu duk abin da suka nema ba tare da wadansu sun san abin da aka yi ba. Amma wannan matakin da suka dauka babu abin da zai haifar sai karin matsalar tsaro da shigar da wadansu cikin ayyukan assha. Dalili shi ne, wani sai dai a kashe shi in aka ce za a daukar masa dukiya, domin nan ya dogara. Amma mutum ya bar dukiyarsa ya dawo da safe ya ga babu ita, ai sai wani ikon Allah zai hana shi shiga cikin mawucin hali,” inji shi.

Ya ce “Ke nan maimakon samun sauki sun taimaka an kara jefa al’umma cikin bala’i. Kuma mu a kungiyance ba mu goyon bayan shigo da kayan nan da ake yi domin suna karya mana tattalin arziki, amma in har an bari an shigo da kayan cikin gari, to a kyale a sayar. Domin an ce babu inda mai aro za shi ba tare da sanin mai kaya ba.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kakakin Hukumar Kwastam a Katsina Theophilus Duniya kan lamari ta rubuta masa sakon tes, amma har lokacin hada wannan rahoto bai amsa ba. Sai dai Aminiya ta ji shi yana cewa a wani shiri da aka yi da shi mai taken, “Daga Jami’an Tsaro” da gidan rediyon Bision da ke Katsina ya gabatar a kwanakin baya, yana cewa suna da waranti wanda ya ba su damar zuwa ko shiga ko bude duk wani wurin da suke zargin akwai kayan da aka haramta shigo da su domin su kwashe su kai ofishinsu, inda wannan waranti ya ba su damar zuwa a ko’ina kuma a kowane lokaci.

Sai dai Kakakin bai fito ya yi wani bayani gamsasshe ba a kan yin amfani da bindiga a cikin gari ko a kan wanda suka biyo. Illa dai ya ce wannan tsari gwamnati ta bullo da shi ne domin habaka tattalin arzkin kasa.