✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kwayoyin ‘cuta’ da muke amfana da su

Wasu za su yi mamakin a ce akwai kwayoyin cutar da kuma ba sa saka mana wata cuta sai dai ma su amfanar da mu.…

Kwayoyin Fungus na YisWasu za su yi mamakin a ce akwai kwayoyin cutar da kuma ba sa saka mana wata cuta sai dai ma su amfanar da mu. Wato wadannan kwayoyi sai dai su taimaka wa jikinmu maimakon su sa mana wata matsala. Shin to me ya sa ake ce musu kwayoyin cuta, tunda ba za su sa wata cuta ba? Ana ce musu kwayoyin cuta saboda su ma ’yan uwan kwayoyin cuta ne, wato danginsu duka daya ne, kuma za su iya sa cuta ga wanda garkuwar jikinsa ta karye. Don haka an yi wannan rubutu ne domin kawai a san da wadannan kwayoyi da ba sa cutar da mu, ba wai don kada mu ci gaba da tsabta da taka-tsan-tsan da ’yan dabarun da muke ta nanatawa don kariya daga miyagun kwayoyin cuta ba.
A 1920 ne wani likita dan kasar Ingila mai suna Aledander Fleming ya fara gano maganin kwayoyin cuta na bacteria, yayin da yake bincike a kan wasu kwayoyin cuta na daban, wato kwayoyin fungus. A lokacin da yake wannan aiki ne ya lura kwayar bacteria fa ba ta son ta zo kusa da wadannan kwayoyi na fungus. Don haka sai ya kawo wadannan kwayoyin fungus ya zuba su a kan na bacteria, nan da nan kuwa na bacteria suka mutu murus. Daga nan ne fa aka gano maganin kwayar bacteria ta hanyar karantar halitta da noma ita wannan kwayar fungus. Wato dai magungunan farko na kwayar bacteria da wata kwayar cutar aka yi su. Ka ji inda kwayar cuta ke maganin wata kwayar cuta. Amma a yanzu dai sarrafa maganin ake a cikin dakin bincike domin ya yi kama da shi sinadarin cikin fungus din da bacteria ba ta so. To irin wadannan aikin amfani akwai su da dama. Bari mu lissafo wasu daga cikinsu:
kwayoyin da ke cikin hanjinmu: Akwai kwayoyin cuta a cikin babban hanjinmu da suke taimaka mana wajen kamawa da kashe wasu miyagun kwayoyi. Ban da wannan akwai kuma wadanda suke sarrafa mana wani sinadarin bitaman na rukunin K, wanda ke aikin tsaida jini idan mutum ya ji rauni, da masu sarrafa mana wasu sinadaran bitaman na rukunin B. akwai kuma masu taya mu murza abinci a babban hanji. Misali, idan aka ci abinci mai tauri, wanda bai narkewa gaba daya, to da ya zo babban hanji sai wadannan kwayoyi su murje shi su mai da shi iska, wadda takan zama tusa. Shi ya sa wasu kalar abinci masu tauri kamar wake da doya ke sa wasu mutane yawan tusa. To hakan taimako domin gara su zama iska da a ce su sa ciki ya yi kabe-kabe, a rasa yadda za a yi da shi.
kwayoyin da ke cikin abincinmu: Wadannan irin kwayoyi akan same su ne a wasu irin abinci da muke ci yau da kullum. Wato abincin da muke ci yau da kullum su ma fa duk yadda ka yi sai an samu kwayoyin halittu. Wadannan abinci su ne madarar yagot, chukwi da shayin coffee, awara, kabeji da sauran ire-irensu. kwayoyin da aka fi samu a ciki su ne na bacteria, masu shiga cikin hanji su kashe wasu kwayoyin. Su ne masu samar da wadancan sinadarai da muka lissafa a sama. Dadin dadawa kuma sukan daidaita yadda ciki ke tace abinci.
Yayin da mutum ya faye shan magungunan kashe kwayoyin cuta ba tare da shawarar ma’aikatan lafiya ba, wadannan kwayoyi su ma suna mutuwa ta yadda zai rasa wadannan amfani da suke samar masa.
kwayoyin da ake wasu abincin da su: Misalin wadannan su ne kwayar yeast (yis) wata kwayar fungus ce wadda ake kwaba fulawa da ita. Wadannan kwayoyin ne ake sayarwa a cikin leda a kasuwa, kuma idan aka sa a fulawa take kumburowa. Su aikinsu ke nan, su kumbura duk wani abu da suka shiga. Fulawar da ba a sakawa yis ba tafi wadda aka karawa yis nauyi. Wato kamar a ce burodin da ba a sa masa yis ba, ya fi wanda aka sa wa nauyi. To idan aka gasa su kwayoyin sai su mutu, wasu kuma su dan suma. Shi ya sa idan aka bar burodi misali ya dan yi kwanaki yake nuna hunhuna, wadda ke nufin wadannan kwayoyin fungus sun farfado ke nan.
kwayoyin da ake allurar riga-kafi da su: Da yawa daga cikin kwayoyin da ake hada ruwan allurar riga-kafi da su kwayoyin cuta ne na birus wadanda yawanci ba su da magani sai dai riga-kafi. Su wadannan kwayoyin birus ana rage musu karfi ne ko kuma a nakasa su ta yadda ba za su mutu ba kuma ba za su sa ciwo ba, amma za su iya sa garkuwar jiki ta kera kwayoyin da za su yake ta, wadda shi kawai ake bukata a riga-kafi.
kwayoyin da ke cikin kasa: Akwai kwayoyin cuta a cikin kasar da muke takawa. Kadan ne kawai a cikin wadannan kwayoyi suke sa mana cututtuka (wato irinsu kwayar cutar tatanas). Sauran sukan taimaka wajen ruguza wadansu abubuwa da ba ma so su taru a cikin kasar. Misali, akwai kwayoyin bacteria masu cin leda, wadda idan ta taru a kan kasa takan iya shekaru aru-aru idan ba kwashe su aka yi ba. Akwai kuma masu cin bayan gida, su mai da shi kasa. Wannan ne kan sa wasu nau’in masai ko shadda irin na zamani ke da rariya masu shiga cikin karkashin kasa (soak-away), ta yadda kwayoyin cuta za su maishe su kasa. Akwai kuma masu cin danyen mai irin wanda ya zube a wuraren hakar mai. Wato da za a bar hakar mai a wasu wuraren hakar mai wanda ya baci, wata rana za a zo bayan ’yan shekaru a nemi dagwalon a rasa, kwayoyin cuta duk sun lashe man.

LAFIYAR MATA DA YARA

Na gama awon ciki fiye da wata guda ke nan ban haihu ba. Ya zan yi?
Daga Marwiyya, Kano
Amsa: Abin da ya fi kawowa mai juna biyu zaton ta wuce lokacin haihuwarta shi ne rashin iya kirgen wata. Ya kamata a ce mace mai juna biyu ta rike kwanakin cikinta ta kuma iya lissafa ranar haihuwarta. Yadda ake wannan lissafi mai sauki ne, idan dai har mace ta iya rike kwanan watanta, wato ranar da ta fara al’adar da ta yi ta karshe ba ranar da ta gama ba. Daga wannan rana ake fara kirgen watannin ciki. Daga nan sai ki kara wata tara da sati daya wato kwana bakwai, to ranar kwanan watan da kika samu ana kyautata zaton ita ce ranar haihuwarki. Misali, a ce ranar 2 ga watan Janairu kika fira al’adarki ta karshe to idan kika kara wata tara da sati daya a kan wadancan kwanaki za ki samu kwanan wata 9 ga watan Oktoba. To kin ga wannan rana ta tara ga wata ita ce a kimiyyance ake ganin za ki haihu a cikinta. Wasu sukan ce ki rage kwana biyu ko ki kara biyu, wato za ki iya haihuwa 7 ga wata ko 5 ga wata.
Idan kuma ba za ki iya wannan lissafi ba, kwanakin ciki na farko, wato da kin ji alamu na juna biyu za ki iya zuwa asibiti a duba ki a ba ki gwajin fitsari da hoton ciki don tabbatarwa ko cikin ne. To wannan hoto na farko shi ne ke nuna ranar da ake sa ran za ki haihu. Duk wani hoto da za ki sake dauka wanda ya biyo bayan wannan zai ba da wata ranar haihuwar daban, amma na farkon nan dai shi ya fi kusan zama daidai. Idan kuma tun farko ma ba a yi hoton ba, kuma ba ki rike lissafin watan ba, to dole ne a yi hoton a tabbatar miki cewa e wannan ciki fa ya wuce wata tara. Da zarar an tabbatar da haka sai a garzaya asibiti.
Duk matar da ta yi awo a asibiti aka fada mata ranar da za ta haihu to dole idan ranar ta zo ba ta haihu ba ta koma asibitin. Wasu sukan fada cewa idan ba ki haihu ba, bayan ’yan kwanaki to ki koma wato idan kika wuce sati 39 kika fara shiga sati 40 wato watan goma.
Likita, an ce jarirai ba sa gani, to idan haka ne wata nawa suke yi kafin su fara gani?
Daga Asiya
Amsa: Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce hankali ne ke gani ba ido ba. Domin kwakwalwa ce ke da alhakin sarrafa gani, ido shi mudubi ne kawai. Mutum zai iya kasancewa idonsa rangadau amma idan wurin da ke sarrafa gani a kwakwalwa na da matsala ba zai iya ganin komai ba.
Kina ina kuma makahon da bai taba gani ba ya shafa tinkiya ya ce tinkiya ce, ya kuma shafa kujera ya ce kujera ce, ya ji kanshin tuwo ya ce tuwo ne? Hankalinsa ya ba shi.
Wato dai jariri na gani daidai da hankalinsa. kwakwalwarsa na sarrafa masa duk abin da idanunsa suka gani daidai hankalinsa da shekarunsa. A watannin farko sun fi gane fuskar mahaifiyarsu, kafin daga bisani suna girma suna gane abubuwan da ke kewaye da su.