✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyaftin din kulob din Ajad ya samu matsala a huhu

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Ajad da ke Holland ya tabbatar wa duniya cewa kyaftin dinsa Siem de Jong ya samu…

Kyaftin din Ajax Siem de JongA ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Ajad da ke Holland ya tabbatar wa duniya cewa kyaftin dinsa Siem de Jong ya samu matsala a huhunsa bayan Likitoci sun gudanar da bincike a kansa.
De Jong, mai kimanin shekara 24, zai shafe kimanin mako shida ba tare da ya buga kwallo ba saboda aikin da za a yi masa.  Hakan ta sa ba da shi za a fara fafatawa a kakar wasa ta bana ba.
Wata sanarwa da kulob din ya fitar a kafar sadarwarsa ta ce :”A ranar Litinin da ta wuce ne Likitoci suka gano akwai matsala a huhun  kyaftin dinmu De Jong don haka ana sa ran zai shafe kwanaki a asibiti don a yi masa aiki kuma zai shafe kusan mako shida ba tare da ya yi wasa ba”.
“Sai dai ba a tabbatar da takamaiman lokacin da dan kwallon ya samu wannan matsala ba, amma dai zai shafe akalla mako shida yana jinya”, inji sanarwar.
Haka kuma dan kwallon ya tabbatar da labarin a kafar sadarwarsa ta Twitter inda ya ce “na samu matsala a huhu kuma zan shafe makonni ba tare da na buga kwallo ba”.