✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyaftin Tijjani Balarabe: Rayuwar sojan ‘da ya kitsa’ kashe ’yan sanda da tserewar Wadume a Taraba

Duk da sunansa ya yi tambari a ko’ina a kuma lebban kowane dan Najeriya, sannan hotonsa ya mamaye kafofin sada zumunta na zamani, amma ba…

Duk da sunansa ya yi tambari a ko’ina a kuma lebban kowane dan Najeriya, sannan hotonsa ya mamaye kafofin sada zumunta na zamani, amma ba kowa ya san yadda rayuwar Kyaftin Tijjani Balarabe take ba kafin badakalar  Jihar Taraba, wadda ta sa sunansa ya  ja hankalin jama’a a cikin ’yan makonnin nan. Aminiya ta yi cikakken bincike a kan rayuwarsa tun yana farar hula da lokacin da yake kurtun soja har zuwa lokacin da likafarsa ta ci gaba ya zama hafsan soja. Da kuma sauran abubuwa da suka shafi sabon gidansa da yake ginawa da kuma sha’awarsa ta yin kasuwanci, wacce ta sanya ya fara gina gidan burodi.

A farkon 1990, a Unguwar Tudun Fera da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa, an samu dimbin samarin da suka gama makarantar sakandare wadanda suke zaman jiran sakamakonsu ya fito, don haka koyaushe za ka same su suna wasan kwallon kafa a kan layi don debe kewa. A cikinsu ne aka samu Kyaftin Tijjani Balarabe, wanda yanzu sunansa ya mamaye kafafen watsa labarai sakamakon zargin da ake yi masa na bai wa wadansu sojoji da ke aiki a Bataliya ta 93 ta sojan Najeriya da ke Taraba umarnin bude wuta a kan ’yan sandan da suka kamo wani da ake zargin shahararren mai garkuwa da mutane ne mai suna Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume.

Bude wutar, ya jawo hallaka wadansu kwararrun ’yan sanda uku wadanda suka yi fice wajen kama masu manyan laifuffuka a fadin Najeriya. Sannan wadansu shida suka samu raunuka a ranar 6 ga Agustan bana.

Wannan lamari ya haifar da yanayi na shigar cacar-baka a kafafen watsa labari a tsakanin hukumomin soja da na ’yan sanda, musammn yadda jami’an sojan suka bayyana ’yan sandan da abin ya shafa a matsayin wadanda ake zargi da garkuwa da mutane a lokacin da suke ba da bayanin cewa soja sun samu ‘kiran neman taimako ne’ bayan da aka yi zargin an sace wani mutum.

Lokacin da yake nuna damuwarsa game da lamarin, Shugaba Buhari take ya bai wa Babban Hafsan Sojin Najeriya umarnin ya kaddamar da bincike a kan abin da ya auku.  Rundunar ’Yan sanda ta Kasa ta sake kama Wadume da ake zargi wanda da farko sojin suka kubutar da shi, sun kamo shi a wata maboyarsa da ke Kano kimanin tafiyar kilomita 700 daga inda abin ya faru a ranar Litinin 19 ga Agusta.

Yadda Tijjani ya shiga aikin soja

Kyaftin Tijjani ya girma a Jos ne a tsakanin 1980 zuwa 1990, kamar yadda Aminiya ta gano, kuma shi sananne ne a cikin tsaransa da matasan da ya girma a Unguwar Tudun Fera da ke garin Jos. Akan yi masa lakabi da suna Tije wadansu kuma su kira shi da  Danfari. A 1992/1993, matashin yana daya daga cikin samarin da suka yi sha’awar shiga aikin soja. Wani soja da ya san lokacin da ya shiga aikin soja ya ce Tije ya fara shiga soja ne a cikin ayarin sojan da ake dauka a kai-a kai a 1993, kafin Shugaban Kasa na wancan lokaci, Janar Ibrahim Babangida ya kaddamar da Rundunar National Guard a shekarar ta 1993.

Direban manya hafsoshi

A nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.