✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyanwa ta makale a injin mota ta yi tafiyar mil 40 da ita

Wata kyanwa ta rayu bayan an yi tafiya mai nisan mil 40 da ita a makale a cikin injin mota (bonet), wanda hakan y asa…

Wata kyanwa ta rayu bayan an yi tafiya mai nisan mil 40 da ita a makale a cikin injin mota (bonet), wanda hakan y asa ta samu munanar kuna a jikinta.

Kyanwar mai suna Chi mai shekara daya ta makale a gurbin da ke kusa da injin motar wani makwabcin wanda ya mallaki kyanwar da ke birnin Brighton, a Karamar Hukumar East Sussed a Ingila.

Wanda ta mallaki kyanwar mai suna Kaylie Banks, mai shekara 30 bayan ta dawo gida daga wurin aiki ta nemi kyanwarta Chi, amma ba ta san inda take ba, hakan ya sa ta damu ta fara tambayar mutanen unguwarsu kan taimaka mata don gano inda kyanwar ta shiga.

Wanda kyanwar ta makale a cikin motarsa ya hadu da wanda ta mallaki kyanwar, inda ya bayyana mata cewa yana cikin binciken motar sai ga kyanwa a cikin bonet na motar. Wadda ta mallaki kyanwar ta yi mamaki kan yadda kyanwar ta rayu duk da zafin injin da ke cikin motar bayan an yi tafiyar mil 40. A nan take Kaylie, ta ciro kyanwar jikinta duk zafin injin mota tare da raunukan da ta ji.

Kaylie, ta kara da cewa, bayan ta dawo daga wajen aiki ta duba ko’ina  ba ta ga inda kyanwar ta yi ba. “Sai da na bincike ko’ina a cikin gidan amma ban ganta ba. Sai na kwankwasa dakin makwabcina, a nan yake fada mini cewa, wata kyanwa ta makale masa a cikin bonet din mota,” inji ta. Kyanwar dai tana bukatar a yi mata tiyatar raunin kunar da ta ji a jikinta, amma a hankali yanzu haka tana samun sauki.

A yanzu haka an kai kyanwar asibitin jinyar kyanwa na PDSA’s  da ke birnin Brighton.

Wata likitar dabbobi ta asibitin mai suna Sadie Reece, ta ce “Kyanwa Chi ta samu munanan raunuka akwai bukatar an wanke raunukan da ta samu sannan a ba ta maganin rage radadin  raunin da ta samu.

Mai magana da yawun Asibitin PDSA, ta ce bayan an kammala yi wa kyanwar magani ta samu lafiya za ta iya zuwa gida da kafafunta, sai dai an manna mata wasu abubuwa a jikinta don kare ta daga raunin da ta ji, tana numfashi da kyau kuma akwai fatan za ta samu cikakkiyar lafiya nan gaba kadan, inji ta.